Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta lashe kofin Carabao Cup a karo na 10 bayan da ta samu nasara akan abokiyar karawarta Chelsea a filin wasa na Wembley da ke birnin Landan.
An shafe mintuna 127 ana fafata kwallo kafin kyaftin din Liverpool Virgil Van Dijk ya jefa kwallo a ragar Chelsea bayan ya jefa wata kwallon da Kostantinos Tsimikas ya bugo daga bugun kusurwa.
Hakan yasa Chelsea ta kasa lashe kofi daya tilo da tafi damar lashewa a bana yayinda take cigaba da zama a matsayi na 11 a gasar Firimiya Lig ta kasar Ingila.
Talla