Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) shiyyar jihar Legas ta tsare jami’anta 10 bisa binciken wasu abubuwa da suka bata.
An tsare jami’an ne a makon da ya gabata bisa zargin karkatar da wasu kayan aiki da ba a bayyana su ba.
- Wakilin Musamman Na Xi Ya Halarci Bikin Rantsar Da Shugaban Ghana
- Kotun Legas Ta Ki Dakatar Da Shari’ar Emefiele
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, kakakin hukumar ta EFCC, Dele Oyewale, ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan kokarin tsaftace hukumar daga ayyukan cin hanci da rashawa.
In ba a manta ba, hukumar ta sallami jami’anta 27 daga aiki bisa wasu tuhume-tuhume.
An sallami jami’an ne a shekarar 2024 saboda laifuka daban-daban da suka shafi ayyukan zamba da kuma rashin da’a.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp