Babbar hukumar gudanarwa ta kwallon kafa ta Duniya (FIFA) ta canza lokacin da tun farko aka shirya fara gasar cin kofin kasashen Afirka na AFCON zuwa shekarar 2026.
Tun farko, hukumar kwallon kafa ta Afirka CAF ta shirya gudanar da gasar AFCON a watan Yunin shekarar 2025 a kasar Morocco, amma FIFA ta dauki matakin kara watanni 6 kafin a gudanar da gasar.
- Sojoji Sun Musunta Zargin Kashe Jama’a A Kudu Maso Gabas
- Sanata Yari Ya Samar Da Taki Ga Manoman Zamfara A Kan Naira 20,000
Za a jinkirta gasar ne sakamakon yadda aka tsara fara gasar cin kofin duniya na kungiyoyi 32 da aka shirya yi a wannan watan na Yunin shekara mai zuwa kamar yadda FIFA ta tabbatar.
Sakataren hukumar CAF, Veron Mosengo-Omba,ya shaida wa manema labarai cewa za’a gudanar da gasar ta AFCON a farkon shekarar 2026,inda ya tabbatar da cewar za’a shirya komai kafin lokacin.