Jami’an hukumar Hisbah reshen jihar Sokoto sun kama sama da katan 200 na abubuwan da ake zargin barasa ne a babbar tashar mota ta Sokoto.
Kwamandan Hisbah na jihar, Usman jatau ne ya bayyana hakan ya yi da yake baje kolin kayayyakin da ake kwace yayin tattaunawa da manema labarai, ranar Laraba a ofishin Hukumar da ke Sokoto.
Jatau ya bayyana cewa, babu wanda ya fito ya ce kayan da aka kwace mallakin shi ne, saboda haka, hukumar za ta tuntubi kwamishinan shari’a kuma babban lauyan jihar domin sanin matakin da za a dauka na gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp