Hukumar Hisbah ta jihar Katsina ta ce ta lalata kwalabe da suka kai akalla 850 cike da barasa a karamar hukumar Kankara da ke jihar.
Kwamandan Hisbah, Dakta Aminu Usman, wanda aka fi sani da Abu-Ammar, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) a Katsina ranar Litinin din da ta gabata.
Abu Ammar ya ce, shi ne ya jagoranci zubar da kwalaben barasar a ranar Lahadi a Kankara tare da rakiyar jami’an gwamnati. Ya kuma nanata kudurin gwamnatin jihar na yakar duk wani nau’i na lalata a cikin jihar.
Ya kara da cewa, an gano barasar ne a cikin wata mota da ta nufi garin, yayin da wasu kuma an kama su a wuraren da ake sayar da su a cikin karamar hukumar.
Kwamandan ya yi kira ga mazauna jihar da su ci gaba da kai rahoton gidaje da wuraren da irin wadannan abubuwa ke faruwa a yankunansu. Ya kuma bukaci jama’a da su ci gaba da baiwa hukumar goyon baya wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na samar da yanayi mai kyau a jihar.