Hukumar Ilimi A Matakin Farko Ta Jihar Kaduna, SUBEB ta kaddamar da horas da Malaman firamare 8,500 fasahar amfani da kwamfuta don inganta harkar karantarwa a fadin kananan hukumomi 23 da ke jihar.
Babbar Mamba a ofishin jin dadin ma’aikara ta SUBEB, Dr Christy Ayi Aladimerin ta taya Malaman murna da kasancewarsu daga cikin wadanda za su samu horon, inda ta ce, tana fatan za su yi amfani da Ilimin da suka samu ba don amfanin kashin kansu kadai ba har zuwa ga dalibansu.
- Manoman Rani Za Su Samu Tallafin Noma Na Gwamnatin Tarayya Da Kashi 50 Cikin 100
- Kowacce Yarinya Za Ta Samu Ilimi Da Sana’a A Jihar Katsina – Gwamnati
Ta kara da cewa, horaswar tana gudana ne a shiyyoyi Uku da ke fadin jihar – Zariya, Tsakiyar Kaduna da Kafanchan, kuma an zakulo Malaman ne daga duk Kananan hukumomin 23 da ke fadin jihar. Za a yi mako guda ana horas da Malaman inda aka fara daga yau Litinin 11 ga Watan Disamba, 2023.
A nasa jawabin, yayin da yake kaddamar da horas da Malaman, Babban Sakataren zartaswa na SUBEB, Alhaji Tijjani Abdullahi, ya ce, domin cika alkawurran da suka dauka na inganta bangaren ilimi, yasa suka shirya wannan horaswar a karkashin shirin (BESDA) ta yadda Malaman za su iya amfani da kwamfuta wajen bincike da kwarewa don amfanar dalibansu.
Alhaji Tijjani ya bayyana amfanin sanin ilimin kwamfuta a wannan zamani da cewa, ya zama dole musamman a bangaren karantarwa. Ya kuma ja hankalin Malaman da su ci gaba da neman ilimin kwamfuta domin kara inganta karantarwarsu.
“Babban burin da muke son cimmawa a wannan horaswar da muka shiryawa Malamanmu shi ne, mu horas da su amfani da kwamfuta don karantar da dalibai, ta yadda za su iya bincike da neman kayan karatu a intanet.
“Da yawan Malaman da muke da su, za ka lura cewa, kamar suna tsoron taba kwamfuta, duk da cewa suna amfani da manyan salular zamani (Android). Don haka, muna fata Malaman, za su samu horo sosai a fannin amfani da kwamfuta don binciken sabbin kayan karantarwa.” Inji Tijjani
Daga karshe, Babban Sakataren, ya jaddada cewa, za su dunga gudanar da bincike a makarantu domin tabbatar da ganin Malaman suna amfanar Dalibai da Ilimin da suka samu.