Hukumar bunkasa noma da raya karkara ta Jihar Kano (KNARDA), ta kudiri aniyar yashe madatsun ruwa da suke da matsala a daukacin kananan hukumomin da su ke Jihar Kano.
Babban manajan darakta na wannan hukuma, Dakta Faruk Kurawa ya shaida wa wakilinmu haka jim kadan bayan kammala taron da cibiyar bunkasa dabarun noma ta Jami’ar Ahmadu Bello (IAR) ta shirya na ayyukan da ta yi a bara da kuma ayyukan bincike da za ta tunkara a wannan shekara.
- Kotu Ta Ce Za A Ci Gaba Da Shari’ar Ganduje Kan Zargin Aikata Rashawa A Kano
- Hukuma Ta Haramta Bikin Ranar Kauyawa A Kano
Dakta Kurawa ya ci gaba da cewa hukumarsa ta yanke shawarar yashe madatsun ruwan ne domin kara bunkasa noman rani da Jihar Kano ta yi fice a kai a shekaru masu yawa da suka gabata.
Ya kara da cewa wannan aikin tuni Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya amince da shi, wanda ya sa hukumar ta sami kwarin gwiwar yin aiki ba tare da bata lokaci ba.
A game da matsalolin da suka faru ga manoman timatir da albasa kuma, Dakta Kurawa ya ce tuni suka gudanar da bincike na yadda wadannan matsaloli da suke faru ga manoman timatir da kuma albasa. Ya ce sakamakon da suka bankado, za su ba gwamnatin Jihar Kano shawarar na dacewar ta tallafa masu kan asarar da suka tsinci kansu a ciki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp