Hukumar Kwallon Kafa ta Turkiyya ta dakatar da ‘yan wasa 1,024 daga gasar kwararru a wani bangare na binciken da take yi akan laifukan caca a tsakanin ‘yan wasan, hukumar TFF ta ce an tura ‘yan wasan da aka gano suna buga caca akan kwallon kafa, ciki har da 27 daga manyan kungiyoyin kwallon kafa na Turkiyya, zuwa ga Hukumar Ladabtar da Kwallon Kafa ta Kwararru ta kasar (PFDK).
Bayan matakin, an dage wasannin rukuni na uku da na hudu na kwallon kafa ta Turkiyya na tsawon makonni biyu, kodayake za a ci gaba da wasannin a manyan gasanni biyu na kasar, hukumar TFF ta nemi hukumar kula da kwallon kafa ta duniya FIFA da ta kara kwanaki 15 ga lokacin saye da sayar da ‘yan wasa na hunturu domin kungiyoyi su iya magance karancin yan wasa.
- Tinubu Ya Zuba Naira Tiriliyan 1.5 Don Bunkasa Noma Da Kayan Aiki Na Zamani
- Babban Taron Kawancen Sin Da Afirka Ya Nuna Hadin Gwiwa Kan Gudanar Da Tsarin Shugabancin Duniya Na Bai-Daya
Besiktas, daya daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa na Turkiyya, ta fitar da wata sanarwa tana mai cewa an tura yan wasanta biyu zuwa PFDK kuma suna da cikakken sa rai kan rashin laifin ‘yan wasan biyu, rahotanni daga kafofin watsa labarai na cikin gida sun kuma ruwaito cewa hukumomin Turkiyya sun kama mutane takwas, ciki har da shugaban kulob, a wani bangare na bincikensu.
Badakalar ta fara bayyana a kanun labarai a ranar 27 ga Oktoba, lokacin da shugaban TFF Ibrahim Haciosmanoglu ya ce daruruwan alkalan wasa suna da alaka da asusun caca, Haciosmanoglu ya yi ikirarin cewa daga cikin alkalan wasa 571 da ke aiki a lig-lig na kwararru na Turkiyya, 371 suna da asusun yin caca kuma 152 suna yin caca a zahiri.
Ya ce kungiyar ta hada da alkalan wasa bakwai da mataimakan alkalan wasa 15 daga manyan sassan biyu na Turkiyya, da kuma alkalan wasa 36 da mataimaka 94 daga kananan rukunoni, shugaban TFF ya kara da cewa alkalan wasa 10 kowannensu ya buga sama da caca 10,000, Alkali daya ya buga 18,227, yayin da alkalan wasa 142 suka buga wasanni sama da 1,000, wasu alkalan wasa sun buga caca daya kawai.
Kamar ‘yan wasa da masu horarwa, an hana jami’an wasa shiga ayyukan yin caca bisa ga ka’idojin TFF, da kuma na FIFA da hukumar gudanarwa ta Turai (Uefa), masu gabatar da kara na Turkiyya sun bayar da umarnin tsare mutane 21 ciki har da alkalai 17 da shugabannin kungiyoyin kwallon kafa biyu a wani bangare na babban bincike kan yin caca da kuma shirya yadda sakamakon wasa zai iya fitowa.














