Hukumar Kwastam reshen Kano ta samu nasarar tattara kudin shiga na naira biliyan 6.9 a cikin watan Nuwamba na wannan shekarar kamar yadda shugaban hukumar Mista Dauda Ibrahim Chana, ya bayyana ranar Litinin a Kano.
Mista Chana, wanda yake shugabantar jihohin Kano da Jigawa ya kuma lura da cewa “Mun kuma samu nasarar kwace buhunan shinkafar waje guda = 2,817, tayoyin mota = 1,428, jarkan man gyada= 250 da sauran kayayyakin da aka haramta shigowa cikin kasar nan da su.
- Kwastam Ta Kwace Tirelar Shinkafa 13 Da Kayan Naira Bilyan 1.2
- Kwastam Za Ta Rungumi Aiki Da Fasahar Zamani Domin Habaka Harkokinta – Adeniyi
“Sauran kayayyakin da aka kama sun kuma hada da dilan gwanjo 429, katan din man gyada 1,226 na kwayar Tiramadol, da tabar wiwi 470 da kuma katan din taliyar kasar waje guda 1,530.
Ya kuma kara da cewa, hukumar ta dauki muhimman matakai don ganin an samu nasarar kare dukkan ayyukan masu fasa kwauri a sassan jihohin.
Ya ce, a halin yanzu jami’an hukumar na aikin sintiri a iyakar kasar nan ta garin Maigatari da ke karamar hukumar Gumel a Jigawa don kawo karshen masu ayyukan fasa kwauri.
“Muna kuma Shirin tura karin wasu jami’a zuwa yankin karamar hukumar Babura ta Jihar Jigawa.
Daga nan ya nemi taimakon sarakunan gargajiya da dukkan masu ruwa da tsaki wajen fadakar da al’umma a kan illolin fasa kwauri ga tattalin arzikin kasa.