Hukumar Kwastam ta Nijeriya (NCS) da ma’aikatar harkokin tsaron cikin gida ta farin kaya (DSS) sun bayyana shirinsu na inganta hadin gwiwa don yaki da ta’addanci a kan iyakokin kasar musamman masu fasa-kwauri da safarar miyagun kwayoyi.
Wannan yunkurin ya biyo bayan tattaunawar da aka yi a ranar 6 ga Maris, 2025, tsakanin Kwanturola na yankin Oyo/Osun, Joseph Adelaja, da Daraktan DSS na jihar, Mista Rasheed Adelakun, a hedikwatar DSS ta jihar dake Ibadan, jihar Oyo.
- An Rufe Taro Na 3 Na Majalisar CPPCC Karo Na 14
- Kwallon Mata: Nijeriya Ta Nuna Wa Afrika Ta Kudu Kwanji A Pretoria
Sanarwar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da NCS ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Litinin.
Adelaja ya jaddada mahimmancin ƙarfafa musayar bayanan sirri da haɗin gwiwar hukumomi, duba da irin kaifin basira da masu fasa-kwari ke amfani da wasu a ‘yan kwanakin nan wurin cimma muradunsu.
“Masu fasa kwauri na ci gaba da bunkasa a ayyukansu, kuma don tunkararsu yadda ya kamata, dole ne mu hada kai ta hanyar bayar da bayanan sirri don cimma nasarar ayyukanmu,” in ji shi.














