Hukumar Kwastam ta Nijeriya ta ce, ta himmatu kuma za ta kara zage damtse wajen yaki da masu safarar abinci zuwa ketare ba bisa ka’ida ba, domin tabbatar da isasshen abinci ga ‘yan kasar.
Ko’odinetan hukumar ta shiyyar B, Ify Ogbudu ce ta bayyana hakan a lokacin da ta kai ziyarar ban girma ga Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero a fadarsa.Hukumar Kwastam Ta Ɗaura Ɗamarar Yaƙi Da Masu Safarar Abinci Zuwa Ƙetare.
- Marseille Ta Kori Kocinta Gennaro Gattuso Bayan Ya Jagoranci Wasanni 15 Kacal
- Babu Wata Kasa Da Za Ta Tsira Muddin Akasarin Kasashen Duniya Na Cikin Tashin Hankali
Ta tabbatar da shirin hukumar wajen ganin ta raba ton 42,000 na hatsin da gwamnatin tarayya ta amince a raba wa masu karamin karfi.
Ogbudu ta nemi goyon bayan mai martaba sarkin kan muhimman ayyuka da hukumar kwastam ke gudanarwa wajen bin umurnin kudirin gwamnati na kawar da talauci da samar da abinci.