• English
  • Business News
Thursday, October 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hukumar Kwastam Ta Kama Kayan Fasakwari Daban-Daban Har 132 Cikin Kwanaki 60

by Sulaiman
3 years ago
Kwastam

Hukumar Kwastam ta Nijeriya (FOU) shiyyar ‘B’ mai hedikwata a Kaduna, ta ce, ta kwace kayayyaki daban-daban har 132 da akayi fasakwarin su da darajar kudinsu ya kai Naira N690,821,657.94 a cikin kwanaki 60 da suka gabata.

Kwanturola Albashir Hamisu wanda ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai jim kadan bayan baje kolin kayayyakin da aka kwace daga jihohin yankin, ya yabawa rundunar sojin Nijeriya bisa gudunmawar da suka bada wajen samun nasarar bankado masu fasakwaurin.

  • ‘Yan Fasakwari Sun Harbe Jami’in Kwastam, Sun Raunata Uku A Kwara

Ya ce, duk da cewa ’yan fasakwaurin suna amfani da kwarewa, amma duk da haka, hukumar kwastam ta kan iya gano su, kuma za ta ci gaba da kwace kayayyakin su har sai sun daina yi wa Tattalin Arzikin kasa zagon kasa.

Kayayyakin da aka kama sun hada da dilar kayan gwanjo 758 da buhunan shinkafa 749 (50kg) ta kasar waje da wasu buhunan shinkafar kasar waje 65 (25kg) da katan 533 na taliyar kasashen waje da macaroni da kuma katon 473 na kayayyakin magunguna na kasashen waje.

Sauran kayayyakin sun hada da fakiti 70 na tabar wiwi da jarika 59 (5 lita) na man gyada da buhuna 47 na takin kasashen waje (NPK 50:50:50) da gwanjon tayoyin mota 245 da jarkar man fetur 221 (25lita) ) da katan 116 na takalman mata na kasashen waje da jarkar man gyada 10 (25lita).

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin Shugaban INEC

Haka kuma, an baje kolin motoci guda 24 da suka hada da guda 4 da aka yi amfani da su wajen jigilar kayayyakin da kuma motocin hawa 20 da katan 14 na man gyaran jiki na kasashen waje da katan 12 na tabar sigari da buhu 39 na gwanjon takalma da buhu biyu na gwanjon jakunkuna.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara
Labarai

Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

October 16, 2025
Sabbin Ministoci
Manyan Labarai

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin Shugaban INEC

October 16, 2025
Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafa Wa Fursunoni Bayan Kammala Zaman Kurkuku
Labarai

Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafa Wa Fursunoni Bayan Kammala Zaman Kurkuku

October 16, 2025
Next Post
Barazanar Kai Harin Ta’addanci: Buhari Zai Gana Da Hafsoshin Tsaro Yau Litinin

Barazanar Kai Harin Ta'addanci: Buhari Zai Gana Da Hafsoshin Tsaro Yau Litinin

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

October 16, 2025
Shugabannin Kasashe Da Dama Sun Yaba Wa Sin Kan Gudummawar Da Ta Bayar A Fannin Tabbatar Da Daidaiton Jinsi

Shugabannin Kasashe Da Dama Sun Yaba Wa Sin Kan Gudummawar Da Ta Bayar A Fannin Tabbatar Da Daidaiton Jinsi

October 16, 2025
Sabbin Ministoci

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin Shugaban INEC

October 16, 2025
Ɗaga Matsayin Dangantakar Zambia Da Sin Ya Haifar Da Manyan Nasarori

Ɗaga Matsayin Dangantakar Zambia Da Sin Ya Haifar Da Manyan Nasarori

October 16, 2025
Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafa Wa Fursunoni Bayan Kammala Zaman Kurkuku

Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafa Wa Fursunoni Bayan Kammala Zaman Kurkuku

October 16, 2025
Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC

Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC

October 16, 2025
Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC

Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC

October 16, 2025
An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga

An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga

October 16, 2025
Gwamnan Edo Ya Umarci Kwamishinoni Su Riƙa Sanya Hular Tinubu

Gwamnan Edo Ya Umarci Kwamishinoni Su Riƙa Sanya Hular Tinubu

October 16, 2025
Baba-Ahmed Ya Zargi El-Rufai Da APC Kan Haifar Da Rashin Tsaro Don Neman Mulki

Baba-Ahmed Ya Zargi El-Rufai Da APC Kan Haifar Da Rashin Tsaro Don Neman Mulki

October 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.