A ranar Laraba ne Hukumar Kwastam da ke aiki a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas ta ce ta kama kwayoyin Tramadol da darajarsu ta kai Naira biliyan N3.55 da aka shigo da su Nijeriya daga kasar Pakistan da Indiya.
Da yake jawabi a taron manema labarai, shugaban hukumar kwastam na yankin, Kwanturola Muhammed Yusuf, ya kuma bayyana cewa rundunar ta samu naira biliyan N74.28bn na kudin harajin kayayyakin da shigo da su kasar a tsakanin watan Janairu zuwa Oktoba, 2023.
Kwanturola Yusuf ya ci gaba da cewa, an kama haramtattun miyagun kwayoyi ne bisa zargin wuce adadin da gwamnatin tarayya ta amince da shi.
Talla