Kasa da mako guda da lalata kwantenar da ke makare da kwayoyin Tramadol da hodar iblis da sauran miyagun kwayoyi, hukumar kwastam ta samu nasarar cafke wasu haramtattun kayan maye da yawansu ya zarce na biliyan N1.4 a yankin Apapa da ke jihar Legas.
Katon-katon na haramtattun kayan maye da aka kama a cewar reshen hukumar da ke Apapa an sakayesu cikin akwati da aka rufe cikin ababen rufe kayan abinci da zimmar karkatar da hankulan hukumomin domin samun nasarar jigilarsu zuwa inda ake son kaiwa.
- NDLEA Ta Kwace Kwaya Mai Nauyin Kilo 4,520 A Jihar Zamfara
- NDLEA Ta Kwace Tiramol Miliyan 2.7 A Legas
Da ya ke ganawa da ‘yan jarida dangane da kayan da suka kaman, Kwanturolan da ke kula da ofishin kwastam na Apapa, Compt. Yusuf Malanta, ya yi bayanin cewa a ranar 21 ga watan Yulin 2022 ne suka samu bayanan sirri da ke ce musu wata kwantena mai lamba SUDU-7538656 da aka gano na dauke da kayan maye da aka haramta amfani da su cikin abin rufe kayan abinci.
Daga nan ya gargadi masu ruwa da tsaki da su daina Saharanpur miyagun kwayoyi a fadin kasar nan, yana Mai cewa hukumarsu ba za ta sarara wa masu irin wannan aika-aikar ba.