Hukumar lafiya ta ankarar da al’ummar Jihar Neja kan hadarin cutar bakon dauro da ke barazana da kananan yara kallan 1.146.572 ‘yan tsakanin watanni shida zuwa shekaru biyar da haihuwa.
Jami’in kula da annobar bakon dauro na hukumar lafiya, Hassan Musa Abari, ya bayyana amfanin gudunmawar kafofin yada labarai wajen wayar da kan al’umma na amfanin rigakafin.
- Manoman Alkama 200 Za Su Amfana Da Shirin NALDA A Jihar Jigawa
- Kasar Sin Za Ta Kafa Karin Yankunan Misali 29 Na Inganta Shigo Da Kayayyaki Kasar
Abari ya ce yekuwar na da matukar alfanu ganin yadda aka fara samun rahotannin bullar annobar wanda ya yi sanadin mutuwar yara sha takwas a jihar a halin yanzu, domin haka dukkanin mazabu 275 da ke jihar za a gudanar da aikin rigakafi.
Abari ya ci gaba da cewar an zabi wasu makarantun faramare da ake son gudanar da aikin saboda cinkoson dalibai, cudanyar yara waje daya na daga cikin hanyoyin yaduwar annobar, ya bukaci iyayen yara da su goya wa shirin baya saboda kaucewar yaduwarsa ga ‘ya’yansu.
A cewarsa, a babban asibitin gwamnatin tarayya da ke Bida, an samu rahoton bullar annobar ga yara 1,347 cikin watanni takwas kuma goma sha takwas daga cikin yaran da suka yi jinya sun rasa rayukansu a cikin wannan shekarar.
Hukumar UNICEF ta ce gwamnatin jiha ta ba ta umurnin fara aikin kashin farko daga ranar 31 ga watan Oktoba zuwa 7 ga watan Nuwamba, yayin zango na biyu da ya kunshi sauran kananan hukumomi zai fara daga ranar 8 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga watan, wanda ya kunshi Agwara, Bargu da Edati, Magama da Kontagora, Mariga da Mashegu, Rafi, Mokwa, Rijau da Wushishi.
Sauran su ne Chanchaga, Bosso, Paiko da Lapai, Gurara, Suleja, Labun, Munya, Shiroro da Katcha, Bida, Agaie da Gbako.