Tun da aka kafa hukumar a shekarar 1992, NASENI ta ɗora Nijeriya kan turbar masana’antu da dogaro da kai ta hanyar ƙirƙire-ƙirƙire na kimiyya da fasaha da suka kawo sauyi a ƙasar. Idan aka yi la’akari da hurumin sa da aikinta, NASENI ita ce kawai hukumar da aka gina a Nijeriya don gudanar da ayyukan ci gaba a masana’antu. A cikin shekaru da yawa, ta nuna ikon daidaita yaɗuwar fasahohin da aka haɓaka a ciki ko wajen cibiyoyinta, gami da haƙƙin mallaka da aka samu.
NASENI ta tabbatar da cewa an tura fasahohin da aka ɓullo da su a fannonin daban daban da tattalin arziƙin ƙasa, domin samar da kayayyaki da ayyuka ga al’umma.
- Nan Ba Da Jimawa Ba Jirgin Sama Mai Saukar Ungulu Ƙirar Nijeriya Zai Fara Tashi – NASENI
- NASENI Ta Dukufa Kere-kere Domin Kawo Saukin Rayuwa A Nijeriya –Khalil
NASENI ta ƙarfafa ƙudurin ta a ƙarƙashin tsarin Shugaba Bola Tinubu na kawo sabbin abubuwa ga ci gaban masana’antu a Nijeriya. Kwanan nan, hukumar ta ƙaddamar da wani gagarumin ci gaba mai suna ‘Innoɓation Hub’ wanda aka ƙera domin bunƙasa ƙirƙire-ƙirƙire na cikin gida a tsakanin matasa masu hazaƙa don bunƙasa masana’antu, samar da ayyukan yi da rage dogaro ga kayayyakin ƙasashen waje.
Kaddamar da Cibiyar ta kuma tallafa wa masu ƙirƙire-ƙirƙire na Nijeriya. Wani ɓangare nasa shi ne ƙalubalen da aka sa wa suna InnoɓateNaija, wanda aka samar tare da haɗin gwiwar AfriLabs, wanda ke da nufin ɗinke giɓin tallafi ga matasa, da taimakawa tallata fasaharsu, da kuma bunƙasa masana’antu da ci gaban tattalin arzikin Nijeriya. Haɓaka hazaƙar ‘yan ƙasa, waɗanda suka ci gaba Fnnin fasaha na da damar buɗe damar fitar da kayayyaki zuwa ƙetare, da taimaka wa Nijeriya samun kuɗin waje da shiga cikin yankin ciniki Afirka (AfCFTA).
NASENI ta kuma baiwa mazauna babban birnin tarayya Abuja damar samun iskar gas (CNG) a kan farashi mai rahusa a lokacin da ta hada hannu da kamfanin Portland Gas Limited wajen ƙaddamar da tashar iskar gas da ke Kubwa, Abuja, a wani ɓangare na matakan ƙara ƙaimi wajen samar da makamashi a Nijeriya.
Wannan shi ne daya daga cikin martanin NASENI da abokan huldarta don samar da CNG, wannan kuma na daga shirin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na daƙile tasirin cire tallafin man fetur ta hanyar samar da iskar gas mai rahusa.
Manufar ita ce a rage dogaro da na’urorin lantarki da ake shigowa da su daga waje, da inganta dogaro da kai a ɓangaren fasaha, da samar da ayyukan yi. NASENI tana ba da ababen more rayuwa da tallafin manufofin, yayin da ɓangaren da ke kula da masana’antu, yana mai da hankali kan haɗin gwiwa, ƙirƙira da kasuwanci don kafa Nijeriya a matsayin cibiyar fasahar Afirka.
Wannan dabarar da NASENI ta yi ya tabbatar da cewa ba a bar kasar a baya ba a cikin juyin juya halin masana’antu da ke faruwa a duniya a halijn yanzu.
NASENI na zuba jari mai yawa wajen bincike a ɓangaren ayyukan da ake yi na yanayi mai dorewa a Nijeriya domin bunkasa tattalin arzikin ƙasa kamar yadda yake a tsare staren tattalin arziƙin shugaba Bola Ahamed Tinubu.
Hukumar NASENI ta haɗa kai da gwamnatin Jamhuriyar Czech domin raba jimillar dala miliyan 21.7 ga zababbun mutane 11 da za su ci gajiyar ayyukan Delta-2 don fara aiwatar musayar fasahohin zamani zuwa Nijeriya. Shirin Delta-2 shi ne samfurin haɗin gwiwar Hukumar Fasaha ta Jamhuriyar Czech (TA CR) ta hanyar da TA CR ke tallafa wa aiwatar da bincike da haɓaka masana’antu da cibiyoyi masu ƙima. An ƙaddamar da shi ne a cikin shekarar 2021, shirin Delta-2 yana ba da kuɗi kuma yana ba da damar bincike da haɓaka ayyukan ƙirƙire- ƙieƙire a fannoni uku da aka mayar da hankali: aikin gona, ma’adinai, da masana’antu gaba ɗaya.
Samar da famfon ban ruwa mai amfani da hasken rana na NASENI ya kawo sauyi ga harkar noma ta hanyar inganta noman rani. Yanzu haka manoman Nijeriya suna amfana ta hanyoyi daban-daban daga wannan fanfo mai sauƙin gaske wanda ke samar da ingantaccen ruwa na amfanin gona. Manoma za su iya amfani da famfon ban ruwa mai amfani da hasken rana don samar da amfanin gona akai-akai, wanda hakan zai bunƙasa yawan amfanin gona da kuma girbi da yawa a kowace shekara.
Yana sa manoma su rage dogaro da yanayin ruwan sama maras tabbas, don haka yana rage haɗarin gazawar amfanin gona. Yana kawar da dogaro da man dizal ko man fetur don ban ruwa tare da rage hayakin iskar gas da gurɓataccen muhalli. Hakanan za a iya amfani da shi a wuraren da basa tare da babbar hanyar wutaingantaccen hanyar grid ba. Ta hanyar amfani da famfunan ban ruwa mai amfani da hasken rana na NASENI, manoma suna ƙara haɓaka aikin noma sosai, da rage tsadar aiki, da samun ƙarin kuɗin shiga da inganta rayuwa idan aka kwatanta da famfunan ban ruwa masu amfani da man fetur.
Domin wannan ci gaba mai ɗorewa na ci gaban masana’antun Nijeriya da kuma tsara makomar al’ummar ta hanyar dogaro da kai, NASENI ce Gwarzon Kamfanin LEADERSHIP na shekarar 2025.












