Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA sun cafke wani tarin kwayar methamphetamine da aka boye a cikin robar garin kwasta.
Jami’an sun cafke kayan ne acikin wasu kayayyaki da za a kai birnin Landan na kasar Birtaniya ta hanyar kamfanin SAHCO da ke jigilar kaya a filin jirgin sama na Murtala Muhammed (MMIA) da ke Ikeja, Legas.
A ranar Talatar da ta gabata ne jami’an NDLEA suka gano wannan haramtaccen maganin da nauyinsa ya kai kilo 30.10, da darajarsa a kananan kasuwanni ya kai Naira miliyan N567m.
Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, ya bayyana cewa, cikin gaggawa aka kama wadanda ake zargi da hannu kan kokarin fitar da kayan, sune: Nwobodo Chidiebere, Chioma Lucy Akuta da kuma wanda ake zargin shi ne shugabansu, Charles Chinedu Ezeh, wanda aka kama a Sotel Suites, Amuwo Odofin, Legas a ranar Alhamis.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp