Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, sun cafke wani sunkin tabar wiwi mai yawa da aka boye a cikin manya manyan lasifiku a cikin wani kaya da aka shigo da su daga birnin New York na kasar Amurka.
A lokacin da aka bude katafaren akwatunan da aka Sanyo lasifikun da jami’an NDLEA suka kama a shingen shigo da kaya ta NAHCO da ke filin jirgin sama na Legas, bayan bude akwatunan, an kama sunkin wiwi 60 da nauyinsu ya kai kilo 33.5.
Akalla, mutane uku da ake zargi, wakilin jigilar kayan, Akeem Afeez; Manajan kamfanin, Babalola Ayodeji Gboyega da mai karbar kayan, Taiwo Olusegun Anuoluwapo duk an kama su a wani samame da aka yi tsakanin ranar Alhamis 15 ga wata zuwa Juma’a 16 ga Fabrairu 2024.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp