Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA, ta bukaci masu zuba hannun jari a fannin, da su zuba jarinsu, a bangaren Tashoshin Jiragen Ruwa.
Shugaban Hukumar, Dakta Abubakar Dantsoho ya yi kiran a yayin da ya kai ziyarar aiki na duba Tashoshin Jirgin Ruwa ta Onne da ta garin Fatakwal.
- Harajin “VAT” Zai Kara Wa Al’ummar Kasar Nan Kuncin Rayuwa Ne Kawai – Gambo Danpass
- Hukumar NPA Za Ta Sake Farfado Da Tasahar Jirgin Ruwa Ta Burutu
Dantsoho ya kuma bai wa masu son zuba hannun jari a fannin tabbacin cewa, hukumar za ta samar masu da kyakyawan yanyi domin gudanar da aikin su.
Ya sanar da cewa, domin a samu nasarar kara bunkasa fannin, akwai bukatar bangaren kamfanoni masu son zuba jari, so shigo cikin fannin, musamman wajen zuba hannun jari a bangaren kimiyyar zamani.
Dantsoho ya buga misali da babban aikin Tashar ta Onne wacce ta faro shekaru biyar da suka gabata, a matsayin aikin da zai kara habaka ayyukan Tashar Jiragen ruwa a kasar.
A cewarsa, Tashar na da karfin da za a iya sauki manyan Jiragen ruwa da kuma sauran kaya.
Ya kuma bayar da tabbacin cewa, Hukumarsa, za ta samar da kariya da ta dace da kuma samar da kyakyawan yani, ga masu son zuba jari a fanin.
Shugaban ya yi kira ga sauran masu ruwa da tsaki da su shigo cikin fannin domin a kara karfafa jigila ta hanyar amfani da tekuna a kasar da kuma a nahiyar Afirka.
Kazalika, Dantsoho ya sanar da cewa, Gwamnatin Tarayya na shirin kara imganta Tashoshin Jiragen Ruwa na Tinkan da ta Apapa.
Ya jaddada mahimmancin yin amfani da kimiyya wajen kara habaka fannin, inda kuma ya sanar da cewa, Nijeriya na da dimbin yawan alumma da gurare, wanda hakan zai kara bata damar kara bunkasa tattalin arzikin da ake da samu a fannin Tashoshin Jiragen ruwa.
Ya sanar da cewa, wannan ziyarar aikin na daya daga cikin kokarin Hukumar na kara janyo ra’ayin masu son zuba hannun jari a fannin, tare da kuma bai wa masu ruwa da tsaki yin duba ga irin aikin da ake gudanarwa na sake farfado da Tashoshin Jirgen ruwan ta Onne da kuma ta Fatakwal.