Shugaban kasa mai jiran gado, Asiwaju Bola Tinubu, zai ci gaba da karbar Naira miliyan 1 da dubu dari biyu a matsayin albashisa a duk wata kamar yadda shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ke karba.
Tunibun zai ci gaba da karbar albashin a haka idan har ba a rattaba hannu kan kudurin karin albashin zababbu masu rike da kujerun siyasa da manyan ma’aikatan gwamnatin tarayya ya zama doka ba kafin ranar 29 ga watan Mayun 2003 ba.
- Gwamnatin Birtaniya Ta Taya Tunibu Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasa
- Sauyin Kudi: Tunibu Ya Kutsa Kai Wurin Taron Gaggawa Da APC Ta Kira Gwamnoninta A Abuja
Babban shugaban hukumar raba daidai na kasa RMAFC, Dakta Bello Muhammad Shehu, ya bayyana hakan a taron lakcha karo na farko kan tattalin arziki da kuma gabatar da wani Littafi da aka gudanar a Abuja.
Dakta Bello ya ce, gwamnonin na karbar Naira miliyan 1.1 a matsayin albashi duk wata, inda ya bayyana cewa, wasu manyan ma’aikata na hukomomin gwamnatin tarayya, na karbar albashi duk wata da ya dara na shugaban kasa da gwamnonin.
A cewarsa, ” Shugaban kasa na karbar albashin Naira miliyan 1.2 ne duk wata, ina kuma da tabbacin cewa wasu manya a hukomomin gwamnatin tarayya, a duk wata suna karbar albashin Naira miliyan 5, wasu kuma Naira miliyan 2.”
Ya ci gaba da cewa, bai da ce a ce ma’aikacin gwamnatin tarayya na karbar albashin da ya zarce na shugaban kasa ko na gwamoni ba.
A cewarsa, alummar gari ne kawai za su iya kalubalantar hakan, inda ya ce, an yi nazari kan albashin zababbun ‘yan siyasa da na wasu manyan ma’aikatan gwamnatin tarayya da na bangaren Shari’a a shekarar 2008.
Ya ce akwai bukatar a sake yin nazari kan albashin na su, inda ya bayyana cewa, kundin tsarin mulkin Nijeriya da aka sabunta ya bai wa hukumar RMAFC damar yanke albashin zababbun ‘yan siyasa da na manyan ma’aikatan gwamnatin tarayya da kuma na ma’aikatan Shari’a.
Don haka bisa wannan tsarin, hukumar ta fara yin nazari kan albashin zababbun ‘yan siyasa da manyan ma’aikatan gwamnatin tarayya da kuma na bangaren Shari’a.