Kwanturolan hukumar kula da shige da fice ta kasa (Immigration) a jihar Ribas, CI James Sunday, ya misalta ayyukan hukumar a matsayin wanda ke taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa sashen zuba jari a Nijeriya.
Sunday wanda ke magana da ‘yan jarida kan rawar da hukumar ke takawa wajen kyautata tattalin arzikin kasa, ya ce, a matsayinsu na masu kula da shige da fice da iyakokin kasa, aikinsu na da alaka kai tsaye da tattalin arziki, siyasa, tsaro, ilimi, addini da kyautata kiwon lafiya a kasar nan.
- Hukumar Raba Daidai Ta Nijeriya Ta Bukaci A Kara Wa Tinubu Da Gwamoni Albashi
- Sauyin Gwamnati Zai Yi Sanadin Rasa Guraben Aiki 2,585 A Nijeriya
Sannan, da tsarin bin dokokin shigowa ko fita, kula da wadanda za su zo domin zuba jari da masu kawo ziyara cikin kasa.
A kan hakan ne ya misalta jajircewa da kokarin da suke yi a matsayin hanyar da ke kyautata sashin zuba jari a cikin Nijeriya, yana mai cewa jami’ansu sun kware wajen gudanar da aikinsu da ake alfahari da su.
James ya bada misalin yadda suka taka rawa wajen kula da iyakokin kasa lokacin da annobar Korona ya barke a kwanakin baya, ta yadda suka kula da masu shigowa domin tabbatar da wadanda suke dauke da cutar ba su shigo sun yada wa al’ummar Nijeriya ba.
Ya kuma kara da cewa, hukumarsu ta taimaka wa tawagar sojojin wajen yaki da ‘yan ta’adda a shiyyar Arewa Maso Gabas ta fuskacin kula da wadanda aka yi garkuwa da su, agajin gaggawa ga ‘yan Nijeriya, ceto da aikin tallafi ga wadanda lamarin ya shafa da taimaka wa ‘yan gudun hijira a jihohin da suke Arewa Maso Gabas.
Ta fannin zuba jari kuwa, ya ce, hukumarsu ce ke bada izinin shigowa kasa ga masu son zuba jari, da masu kawo ziyara da tabbatar da tsawon lokacin zamansu ko wa’adi wanda ta hakan ana samun bunkasar tattalin arziki sosai.
Baya ga masu zuba jari da masu kawo ziyarar, ya ce, hukumarsu kuma tana kula da masu zuwa Nijeriya a bangaren kwararru wadanda ake kira domin su yi gyara ko aikin kwaskwarima na wasu muhimman abubuwa a cikin kasar nan.
“Hukumar NIS a karkashin jagorancin Kwanturola Janar, Isa Jere Idris, ta narka jami’ai sosai da suke taimaka wa tawagar jami’an tsaro, wadanda suke iyakokin kasa da filayen jiragen kasa da suke kasar nan, wuraren kula da iyakoki, wuraren sintirin ababen hawa a kokarinmu na tabbatar da dakile masu shigowa ba bisa ka’ida ba da tabbatar da tsaron kasa.”
Ya kara da cewa, sannan, an ware kwararrun jami’ai wadanda suke kula da jihohi a matsayin kwanturololin jihohi domin tabbatar ingancin aiki da tsaron kasa da kula da masu shige da fice da tabbatar da jama’a na bin cikakken ka’idar samun izinin zama ko shigowa Nijeriya a kowani lokaci.
A cewar James, suna kokarin tabbatar da jama’a na samun sauki da ingancin samun iznin shigowa ko zama cikin Nijeriya a kan lokaci, don haka ne ya tabbatar da cewa akwai kyakkawar tsari da suke da shi wajen inganta aiki a kowane lokaci.