Hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja, ta markade baburan acaba sama da 1,700 da ta kwace, biyo bayan haramcin gudanar da yin acaba a babban birnin.
Ku tuna cewa Hukumar ta haramta ayyukan acaba ne a cikin garin Abuja a cikin shekarar 2006.
Da yake jawabi ga manema labarai yayin da aka fara nika baburan a kashi na biyu a Wuye a ranar Laraba, Daraktan hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta babban birnin tarayya Abuja, Dr. Abdulateef Bello, ya ce markade baburan zai zama izina ce ga wadanda ke da kunnen kashi.
Ya bayyana cewa sun gudanar da aikin markade baburan na karshe ne a watan Disambar 2021 inda suka markade wasu da dama.