Tun daga shekarar 2023, hukumomin gwamnatin Amurka suke kirkiro labaran jabu, suna ikirarin kungiyar kutsen yanar gizo ta “Volt Typhoon” dake karkashin gwamnatin Sin, ta kai hari kan yanar gizon muhimman manyan ababen more rayuwa na kasar. Sun yi hakan ne da zummar karawa zargin “Sin na kawo barazana ga sauran kasashen duniya” gishiri.
Game da hakan, manema labarai na CMG sun nemi karin haske daga cibiyar yaki da kutsen yanar gizo cikin gaggawa ta kasar Sin a jiya Lahadi, game da shirin yaudara da Amurka ke aiwatarwa na fitar da labaran jabu.
- Xi Jinping Ya Gana Da Firaministan Hungary
- Li Qiang Ya Taya Keir Starmer Murnar Zama Sabon Firaministan Kasar Birtaniya
Binciken da hukumomi masu ruwa da tsaki na Sin suka yi na nuna cewa, hukumomin tsaro na Amurka da suka hada da NSA da FBI da sauran hukumomin leken asiri na kasar ne suka kirkiro kungiyar “Volt Typhoon”, inda kuma mambobin majalisar dokokin Amurka masu adawa da kasar Sin da fadar White House da ma’aikatar doka da shari’a da ta tsaron kasar da ta makamashi da sauran hukumomin gwamnati, suka yi hadin kai wajen gabatar da shi, da zummar yada labaran jabu da sarrafa bayanai.
A cikin wannan shiri, hukumomin leken asiri na Amurka sun yi amfani da ikon hukumominsu wajen sarrafa kamfanoni masu aikin tsaron yanar gizo da sauran hukummomi, da zummar kirkira da yada jita-jita cewa, wai kasar Sin tana kawo barazana a wannan bangare, da yaudarar Amurkawa da mambobin majalisar dokoki, ta yadda za su keta moriyar kamfanonin Sin. Dalilin ke nan da ya sa suke yunkurin tsawaita wa’adin aya mai lamba 702 na dokar sa ido kan leken asirin a ketare wato FISA, wanda aka fi sani da dokar leken asiri ba tare da samun izini daga kotu ba, da kuma neman karin kasafin kudade daga majalisar dokoki don inganta karfin kutse na wadancan hukumomi. (Amina Xu)