Hukumar koke-koken Jama’a da yaƙi da cin hanci ta Jihar Kano ta kama shugaban ƙaramar hukumar Ƙiru, Abdullahi Mohammed, bisa zargin siyar da filin da aka tanadar don gina filin wasa na Kafin Maiyaki ba bisa ƙa’ida ba.
Binciken hukumar ya gano cewa an sayar da filin ga wani kamfani mai suna Mahasum akan sama da Naira miliyan 100. Kakakin hukumar, Kabir Abba Kabir, ya tabbatar da kamen, yana mai cewa asusun Mohammed ya karɓi jimillar Naira miliyan 240 tun daga 1 ga Nuwamba, 2024, lokacin da ya hau mulki, zuwa 27 ga Fabrairu, 2025. Hukumar ta ce tuni ta dawo da kuɗaɗen.
- Gwamnatin Kano Ta Amince Juma’a 28 Ga Fabrairu A Matsayin Ranar Hutun Zangon Karatu Na Biyu
- Zaben 2023: Kwankwaso Ya Cancanta Ya Shugabanci Nijeriya -Zakiru Kusfa
Ana ci gaba da bincike don gano dukkan ɓangarorin da suka haɗa hannu a cinikin filin. Mohammed kuwa yana bai wa jami’an bincike haɗin kai domin tantance gaskiyar lamarin.
Hukumar ta jaddada aniyarta ta tabbatar da gaskiya da adalci, tare da tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifi za a hukunta shi. Mohammed na ci gaba da zama a hannun hukuma yayin da ake ci gaba da bincike.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp