Hukumar yaki da shan maganin kara kuzari yayin wasanni ta duniya wato WADA, mai helkwata a birnin Montreal na kasar Canada, ta ba da sanarwa da yammacin jiya Laraba, inda ta mai da martani ga wani rahoton da ta fitar a ranar.
Rahoton ya nuna yadda hukumar yaki da shan maganin kara kuzari yayin wasanni ta Amurka wato USADA, ta amince wasu ’yan wasan kasar da suka sha maganin kara kuzari su shiga gasa a shekarun da suka gabata, kuma bisa misali, ba a taba ba da sanarwa, ko yin hukunci kan ayyukan keta ka’idojin yaki da shan maganin kara kuzari yayin wasanni ba, wanda hakan ya keta ka’idojin yaki da shan maganin kara kuzari yayin wasanni na duniya, da kuma ka’idojin da USADA ta samar da kanta.
- Shugaban Zanzibar Ta Tanzania: Ba Za Iya Raba Ci Gaban Afirka Da Sin Ba
- Zanga-zanga: Hukumar Kare Haƙƙin Bil’adama Ta Ƙasa Ta Yi Allah-wadai Da Kisan Matashi A Zariya
Dan wasan Amurka mai suna Carl Lewis, wanda ya lashe lambobin zinari a gasar wasannin Olympics guda 9, ya taba bayyana cewa, ko da yake an masa gwajin ingancin shan maganin kara kuzari a bincike guda uku a yayin gasar wsannin Olympics da aka gudanar a Seoul, babban birnin Koriya ta Kudu a shekarar 1988, amma babu hukunci da aka yi masa. Har ila yau, dan wasan Amurka Justin Gatlin, wanda ya taba lashe lambar zinari a gasar gudun mita 100, an taba yi masa gwajin ingancin shan maganin kara kuzari sau biyu, bisa ka’ida, kuma ya kamata a hukunta shi, tare da dakatar da shi daga shiga gasar har tsawon rayuwarsa, amma USADA ta yi “kokarin ba shi uzuri”, a karshe dai ta rage lokacin haramcin shigarsa gasa zuwa tsawon shekaru 4 kawai.
Baya ga misalai da aka nuna a fili, a halin yanzu, WADA tana sane da a kalla misalai guda uku da USADA ta amince da su game da ’yan wasan da suka keta ka’idar yaki da shan maganin kara kuzari yayin wasanni su shiga gasa a shekarun da suka gabata. Kuma USADA ba ta sanar wa WADA wadannan ayyukan da ta aikata ba. (Safiyah Ma)