Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Katsina ta fitar da ranar 15 ga watan Fabrairu na shekarar 2025 domin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar.
Shugaban hukumar zaɓen ta jihar Katsina Alhaji Lawal Alhassan Faskari ne ya bayyana haka a taron manema labarai a Katsina.
- Jirgi Mai Saukar Ungulu Kirar Kasar Sin Ya Kammala Gwajin Tashi Da Sauka A Yanayin Hunturu
- Gwamna Lawal Ya Karɓo Sakamakon Jarabawar WAEC Da Hukumar Ta Riƙe
Alhassan ya ce, sun fitar da ranar 15 ga watan Fabrairun shekarar 2025 ne domin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a jihar Katsina. Duk da cewa, wa’adin mulkin shugabannin da ke kan kujerar, zai ƙare ne a wannan watan da muke ciki (Fabrairu).
A cewar shugaban hukumar zaɓen, wannan yunkurin yana matsayin cika sharuɗa na sashe na 197 na kudin tsarin mulki da aka yi wa kwaskwarima na dokar zabe da ta ce a bada kwana 365 kafin lokacin zaɓe.
Don haka, Shugaban ya yi kira ga hukumomin tsaro da kungiyoyin farar hula da ‘yan jarida da su bada gudunmawar da ta da ce domin samun nasarar wannan zaɓe.
Alhaji Lawal Alhassan yana mai kira da babar murya ga hukumomin tsaro da su yi duk mai yiwuwa wajen ganin an samar da tsaro a yankunan da ake fama da matsalar tsaro a jihar Katsina.