Ma’aikatar Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya, a ranar Juma’a a birnin Makkah ta kaddamar da taswirar aikin hajjin shekarar 2024.
Ministan Hajji da Umrah na kasar Saudiyya, Dr Tawfiq Al Rabiah ne ya kaddamar da taswirar aikin a wani biki da ya samu halartar shuwagabanni da wakilan alhazai a kasar.
- Hajji 2023: Alhazan Nijeriya 6 Sun Rasu, 30 Na Da Tabin Hankali A Saudiyya
- Halin Da Mahajjatan Nijeriya Suke Ciki A Saudiyya
Taron dai an yi shi ne domin nuna kawo karshen aikin Hajjin 2023.
Ya ce nan take za a fara shirye-shiryen Hajjin 2024 tare da mika wa kowace kasa da ta sanar da fara shirye-shiryen.
Al Rabiah ya kara da cewa za a kuma fitar da wasikun tabbatar da adadin maniyyata aikin hajjin 2024 ga kasashen da za su halarci aikin Hajjin.
Ya jero abubuwan da suka fi daukar hankali a taswirar aikin hajjin 2014 da suka hada da gudanar da tarukan share fage daga ranar 16 ga watan Satumba zuwa 4 ga Nuwamba, da shirya taron karawa juna sani na kasa da kasa a ranar 8 ga Janairu, 2024.
Al Rabiah ya bayyana cewa aikin Hajji zai zama na farko da ya kammala dukkan shirye-shirye zai kuma sami damar zabar wurare a Masha’er (Mina, Arafat da Muzdalifah) don aikin Hajjin 2024.
Ministan ya mika godiyarsa ga dukkan hukumomi da ma’aikatan aikin hajji bisa rawar da suka taka a wannan aikin hajjin na shekarar 2023 tare da jaddada aniyar Hukumomin Saudiyya na yi wa Alhazai Bakin Allah hidima ta hanyar da ta dace da hanyar jin ra’ayi daga ma’aikatan aikin hajji da inganta ayyukanta.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa babban abin da ya faru a taron shi ne sanar da wadanda suka lashe lambar yabo ta Labbaikum Hajj Services a shekarar 2023 inda Iraki ta zama mafi kyawun shiri a aikin hajjin na shekarar 2023.
Sauran kasashe kamar Malaysia, Gambia, Bahrain, Singapore, Afirka ta Kudu da Azerbaijan sun yi fice a fannoni daban-daban na ayyukan hajji.