‘Yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, da jam’iyyar PDP, Abubakar Atiku, duk sun yi watsi da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa (PEPC) da ta tabbatar da zaben shugaban kasa Bola Tinubu.
Da yake magana ta bakin tawagar lauyoyinsa karkashin jagorancin Dr Livy Uzoukwu (SAN) bayan zaman kotun a ranar Laraba da dare, Obi ya sha alwashin daukaka kara kan hukuncin da kotun ta yanke.
Tsohon Gwamnan na Anambra ya yi gargadin cewa idan ba a kula ba, za a wayi gari a nemi adalci a hukuncin zabe a kasar a rasa, yana mai jaddada cewa ya kamata a rika gudanar da shari’a a kotu ta asali ba ta wucin gadi ba.
Ya jaddada cewa masu shigar da kara da ba su gamsu da sakamakon zabe ba na iya nema wa kansu mafita saboda yadda suke shan wahala a hannun hukumomin gwamnati da ke da ruwa da tsaki a zabe, kamar INEC.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar a lokacin da yake magana ta bakin tawagar lauyoyinsa karkashin jagorancin Chris Uche (SAN), ya ce hukunci kawai aka yanke masa a kotu amma ba adalci bisa doka ba.
Dan takarar na PDP ya ce ya yi tsammanin za a samu hukuncin da zai karfafa amfani da na’urorin zamani wajen inganta gudanar da zabe, tabbatar da gaskiya da rikon amana ta yadda ‘yan Najeriya za su yi imani da dimokuradiyya.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce bai gamsu da hukuncin da kotun ta yanke ba, kuma ya sha alwashin tunkarar kotun koli domin ta yi watsi da zaben shugaban kasa Bola Tinubu.
Ya ce: “An yanke hukunci, amma ba a yi mana adalci ba. Abin farin ciki, Kundin Tsarin Mulki ya ba mu damar daukaka kara.