• English
  • Business News
Sunday, May 11, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hulda Tsakanin Sin Da Kasashen Yankin Gulf Za Ta Samu Sabon Kuzari

by CMG Hausa
2 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Hulda Tsakanin Sin Da Kasashen Yankin Gulf Za Ta Samu Sabon Kuzari
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci taron kolin kasar Sin da kungiyar hadin gwiwa tsakanin kasashen Larabawa dake yankin Gulf karo na farko a birnin Riyadh, fadar mulkin kasar Saudiyya a ranar 9 ga wata, inda ya gabatar da wani muhimmin jawabi.

Wannan ne dai karo na farko da shugabannin kasar Sin, da shugabannin kasashen mambobin kungiyar suka gana kai tsaye, domin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakaninsu.

  • Sin Da Saudiyya Abokai Ne Na Gaskiya Bisa Manyan Tsare-tsare

Yayin taron kolin, sassan biyu sun tsaida kuduri cewa, za su kafa, da kuma kara karfafa huldar abokantaka tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare, wanda hakan babban sakamako ne da suka samu yayin taron, saboda lamarin ya bude sabon shafin hadin gwiwar sassan biyu.

Kungiyar hadin gwiwa tsakanin kasashen Larabawa dake yankin Gulf, babbar kungiyar siyasa da tattalin arziki ce a yankin Gulf, wadda ke kumshe da kasashe mambobi guda shida, wato Saudiyya, da Qatar, da Kuwaiti, da Oman da kuma Bahrain.

Hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen dake yankin na Gulf, ta fi hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da sauran kasashen dake yankin Gabas ta Tsakiya kyau, sakamakon amincewa da junansu a bangaren siyasa, da zumuncin dake tsakanin al’ummomin sassan biyu, musamman ma a cikin shekaru goma da suka gabata. Bugu da kari, hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu ya samu babban sakamako, har sun daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa da dama, bisa shawarar ziri daya da hanya daya.

Labarai Masu Nasaba

Tawagar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Farko Ta Sin Ta Dawo Daga Abyei Cikin Nasara

An Fara Taron Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Matakin Koli Tsakanin Sin Da Amurka A Geneva

Yanzu haka kasar Sin da kasashen Larabawa dake yankin Gulf, suna fuskantar kalubalen dake gaban dukkanin duniya, musamman ma wajen magance karancin abinci da makamashi, hakan ya sa ya dace su kara karfafa hadin gwiwa tsakaninsu, domin samun ci gaba tare. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Sin: An Samu Karuwar Adadin Cibiyoyin Cajin Ababen Hawa Masu Amfani Da Lantarki

Next Post

Taron Kolin Sin Da Kasashen Larabawa Zai Ciyar Da Huldarsu Gaba Zuwa Sabon Mataki

Related

Tawagar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Farko Ta Sin Ta Dawo Daga Abyei Cikin Nasara
Daga Birnin Sin

Tawagar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Farko Ta Sin Ta Dawo Daga Abyei Cikin Nasara

6 hours ago
An Fara Taron Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Matakin Koli Tsakanin Sin Da Amurka A Geneva
Daga Birnin Sin

An Fara Taron Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Matakin Koli Tsakanin Sin Da Amurka A Geneva

7 hours ago
Sharhi: Sin Da Rasha Suna Sauke Nauyin Dake Wuyansu
Daga Birnin Sin

Sharhi: Sin Da Rasha Suna Sauke Nauyin Dake Wuyansu

9 hours ago
Sin Ta Nemi Indiya Da Pakistan Su Muhimmanta Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali
Daga Birnin Sin

Sin Ta Nemi Indiya Da Pakistan Su Muhimmanta Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali

12 hours ago
Xi Jinping Ya Gana Da Shugabannin Kasashe Daban-Daban A Moscow
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Ya Gana Da Shugabannin Kasashe Daban-Daban A Moscow

12 hours ago
Likitocin Sin Sun Ba Da Jinya Kyauta A Yankunan Karkara Na Saliyo
Daga Birnin Sin

Likitocin Sin Sun Ba Da Jinya Kyauta A Yankunan Karkara Na Saliyo

1 day ago
Next Post
Taron Kolin Sin Da Kasashen Larabawa Zai Ciyar Da Huldarsu Gaba Zuwa Sabon Mataki

Taron Kolin Sin Da Kasashen Larabawa Zai Ciyar Da Huldarsu Gaba Zuwa Sabon Mataki

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Farko Ta Sin Ta Dawo Daga Abyei Cikin Nasara

Tawagar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Farko Ta Sin Ta Dawo Daga Abyei Cikin Nasara

May 10, 2025
An Fara Taron Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Matakin Koli Tsakanin Sin Da Amurka A Geneva

An Fara Taron Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Matakin Koli Tsakanin Sin Da Amurka A Geneva

May 10, 2025
Sharhi: Sin Da Rasha Suna Sauke Nauyin Dake Wuyansu

Sharhi: Sin Da Rasha Suna Sauke Nauyin Dake Wuyansu

May 10, 2025

Kungiyar Malaman Jami’o’i Ta Ba Dalibai 164 Tallafin Karatu

May 10, 2025
Dalilan Da Ke Nuna Malaman Makaranta Na Da Muhimmaci (5)

Dalilan Da Ke Nuna Malaman Makaranta Na Da Muhimmaci (5)

May 10, 2025
Sin Ta Nemi Indiya Da Pakistan Su Muhimmanta Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali

Sin Ta Nemi Indiya Da Pakistan Su Muhimmanta Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali

May 10, 2025
Xi Jinping Ya Gana Da Shugabannin Kasashe Daban-Daban A Moscow

Xi Jinping Ya Gana Da Shugabannin Kasashe Daban-Daban A Moscow

May 10, 2025
Ra’ayin Al’umma Game Da Iyaye Masu Furta Muggan Kalamai A Kan ‘Ya’yansu

Ra’ayin Al’umma Game Da Iyaye Masu Furta Muggan Kalamai A Kan ‘Ya’yansu

May 10, 2025
Wayar Salula Na Dab Da Kai Mu Wutar Jahannama

Wayar Salula Na Dab Da Kai Mu Wutar Jahannama

May 10, 2025
Martanin Kwankwaso Ga Kawu Sumaila Da Sauran Masu Ficewa Daga NNPP

Martanin Kwankwaso Ga Kawu Sumaila Da Sauran Masu Ficewa Daga NNPP

May 10, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.