Mahukuntan kwastam na lardin Hunan na tsakiyar kasar Sin sun bayyana cewa, a cikin watanni hudun farko na shekarar 2025, adadin kudin kayayyakin da ake fitarwa daga Hunan zuwa kasashen Afirka ya kai yuan biliyan 8.65, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.2, wanda ya karu da kashi 6.3 bisa dari a mizanin shekara-shekara.
A cewar bayanan da suka fito daga hukumar kwastam ta Changsha, babban birnin lardin Hunan a jiya Jumma’a, kayayyakin injuna da na lantarki da Hunan ta fitar zuwa kasashen Afirka su ne ke da kaso 53.2 bisa dari na adadin kudin kayan da ake fitarwa zuwa kasashen Afirka, da ya kai yuan biliyan 4.6, wanda ya karu da kashi 11.3 bisa dari a mizanin shekara-shekara.
- Mohamed Salah Ya Zama Gwarzon Ɗan Wasan Firimiyar Ingila Na Bana
- Tsokaci Kan Yadda Wasu Matasa Ke Yin Aure Ba Tare Da Sana’a Ba
Kayayyakin “Sabbin fasahohi” da suka kunshi motocin lantarki, da batura masu amfani da hasken rana, da na ma’adanan lithium, duka an samu habakar fitar da su zuwa Afirka, wanda bangarensu ya karu da kashi 747.1 cikin dari a mizanin shekara-shekara zuwa jimillar yuan miliyan 270.
Tun daga watan Disamba na shekarar 2024, kasar Sin ta aiwatar da manufofin soke haraji ga kasashe 33 masu karancin ci gaba a Afirka. Kuma a cikin watanni hudun farko na bana, kayayyakin da Hunan ta shigo da su daga wadannan kasashe 33 sun kai adadin kudin Sin yuan biliyan 3.68, wanda ya karu da kaso 27.1 bisa dari a mizanin shekara-shekara.
Afirka ta Kudu ita ce babbar abokiyar kasuwanci ta Hunan a yankin Afirka a tsakanin wannan lokacin. Kasuwancin Hunan da Afirka ta Kudu kadai ya kai fiye da kashi 1 cikin kashi 5 na yawan cinikin da yankin ke yi da Afirka a tsakanin lokacin. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp