Daga ranar 5 zuwa 10 ga watan Mayu, shugaban kasar Sin Xi Jinping, zai yi ziyarar aiki a kasashen Faransa da Serbia da Hungary.
Yayin wata tattaunawa a baya baya nan da kafar CMG, ministan harkokin wajen Hungary Szijjarto Peter, ya ce a bana Sin da Hungary za su cika shekaru 75 da kulla huldar diplomasiyya, kuma Hungary na sa ran ziyarar shugaba Xi Jinping a kasar, za ta bude wani sabon babi a dangantakarta da Sin. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp