Gidauniyar SCPHPC da ke a Jihar Kaduna, ta taimaka wa masu fama da larurar amosanin jini da rigunan sanyi guda 300 don kare lafiyarsu daga kamuwa da matsalolin sanyi.
Shugabar gidauniyar, Hajiya Badiya Magaji ce, ta jagoranci raba rigunan a ofishinta da ke a anguwar Badarawa a Jihar Kaduna.
- Adamawa: Kotun Koli Ta Sanya 29 Ga Janairu Don Sauraren Kara
- Jariri Ya Yi Batan Dabo A Asibitin Waziri Gidado Da Ke Kano
Badiya, a hirarta da LEADERSHIP Hausa jim kadan bayan rabar da rigunan ta ce, ta raba ne musamman ganin cewa, lokacin sanyi na daya daga cikin lokutan da masu larurar ke fuskantar kalubale.
A cewarta, “Tun kusan shekara 10 da ta kirkiro gidauniyar nan, duk shekara muna raba wa masu larurar da rigunan sanyi.”
Kazalika, Badiyya ta yi kira ga masu hannu da shuni da su rinka taimaka wa gidauniyar musamman da magunguna don ragewa masu fama da larurar radadin halin da suke ciki.