Kasar Sin ta samu bunkasuwa a kasuwannin saya da sayarwa, yayin hutun bikin Qingming na kwanaki uku da aka kammala a ranar Asabar, inda aka samu yawaitar mutane da suka ziyarci wuraren yawon bude ido da tumbatsar harkokin saya da sayarwa.
Alkaluma daga ma’aikatar al’adu da yawon bude ido sun nuna cewa, adadin wadanda suka yi balaguro a lokacin hutu a sassan kasar Sin ya kai kusan miliyan 119, wanda ya karu da kashi 11.5 bisa dari idan aka kwatanta da na shekarar 2019.
Yawan kudaden da suka shigo na yawon bude ido na cikin gida a cikin wannan lokacin ya kai Yuan biliyan 53.95 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 7.6, wanda ya karu da kashi 12.7 cikin dari idan aka kwatanta da na shekarar 2019.
Kasar Sin ta samu tafiye-tafiyen masu shigowa yawon bude ido miliyan 1.04 da kuma masu fita yawon bude ido 992,000 a lokacin hutun, wanda ya yi kusa da yawan tafiye-tafiyen da aka yi a daidai wannan lokacin a shekarar 2019.
A lokacin hutun, an samu karuwar saya da sayarwa, wanda ke nuna kuzarin tattalin arzikin kasar. A cewar bayanai daga Meituan, babban dandalin kasuwancin yanar gizo, matsakaicin adadin saya da sayarwa da aka yi a kowace rana ta dandalin a duk fadin kasar ya samu karuwa mai ban mamaki da kashi 39 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin na bara. (Yahaya)