Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya tabbatar wa masu zuba jari na duniya cewa ƙofar jihar Zamfara a buɗe take ga zuba jari.
Gwamnan da sauran manyan mutane sun halarci taro karo na biyar na gwamnatocin ƙasashen yankin Afirka (AfSNET) da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata a birnin Algiers na ƙasar Aljeriya.
- Kasar Sin Ta Samar Da Kaso 30 Na Jimillar Kason Ci Gaban Masana’antun Duniya A Tsakanin 2021 Zuwa 2025
- Xi Jinping Ya Aika Da Sakon Taya Murnar Bude Taron Cifit Karo Na 25
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya ce, taron ya samu halartar gwamnonin jihar Ogun, Dapo Abiodun, da Kenneth Makelo Lusaka na gundumar Bungoma ta Kenya da dai sauransu.
An samu damar tattauna muhimman abubuwa a babban taron kamar hanyoyin zuba jari a jihohin Ogun da Zamfara na Nijeriya da kuma yankin Bungoma na ƙasar Kenya.
Manyan mambobin kwamitin sun tattauna damarmakin zuba jari a jihohin Ogun da Zamfara a Nijeriya yankin Bungoma na Kenya.
A jawabin sa ga masu zuba hannun jari a duniya, Gwamna Lawal ya jaddada cewa gwamnatin sa ta himmatu wajen sauya labarin Zamfara daga ƙalubale zuwa wani babban matsayi mai cike da damarmaki.
“Gwamnatina ta himmatu wajen samar da ingantaccen yanayi da ɗorewar yanayin zuba jari. Ina nan a yau a matsayin abokin tarayya, a shirye nake na ba ku cikakken haɗin kai don buɗe hanyoyin jin daɗin gare mu duka.
“Don magance matsalolin da suka taso, muna neman haɗin gwiwa a muhimman fannoni don aiwatar da ayyukan zuba jarinmu yadda ya kamata.
“Muna buƙatar masu ba da kuɗi, irin su Afreximbank, don samarwa da sauƙaƙe kayan aiki kamar garantin bashi, inshorar haɗari na siyasa, da wuraren musayar kuɗi. Waɗannan kayan aikin suna da muhimmanci don rage haɗarin da aka sani yayin da suke jawo hankalin manyan ayyuka da haƙar ma’adinai.
“Muna maraba da goyon bayan cibiyoyi don inganta iya aiki a tsakanin hukumomin jihar mu, musamman wajen sabunta rajistar filaye, horar da ƙungiyar haɓaka jarin mu daidai da matakin duniya, da aiwatar da tsarin fasahar zamanidon samar da izini na gaskiya da inganci.”
Gwamna Lawal ya ci gaba da cewa, bayan tarin zinari da jihar Zamfara ke da shi, jihar na da ɗimbin albarkatun da ba a iya amfani da su ba, waɗanda suka haɗa da tagulla, lithium, tantalite, da granite.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp