Alamu masu karfi na nuna cewa tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), zai iya shiga cikin rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar adawa ta PDP.
LEADERSHIP ta rawaito cewa tsohon shugaban na Nijeriya zai yi wata ganawar sirri da dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, da kuma wasu gwamnonin jam’iyyar biyar da aka fi sani da G-5 a Minna, babban birnin jihar Neja ranar Juma’a.
- Yanzu-Yanzu: Wike Ya Jagoranci Tawagar G-5 Don Ganawa Da Gwamnan Bauchi Bayan Sulhunsa Da Atiku
- Wike: “Yakin Neman Zabe Ne Yanzu A Gaban Mu” – Rundunar Yakin Neman Zaben Atiku
Ganawar na zuwa ne kwanaki uku bayan da IBB ya kuma karbi bakuncin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da tawagarsa a gidansa da ke Minna.
Majiyoyi sun nuna cewa matakin na baya-bayan nan na sasantawa kan shigar IBB, da alamun wani tsohon babban jami’in leken asiri na soja ne da wasu masu ruwa da tsaki daga Arewa masu goyon bayan Atiku ne suka shirya hakan.
A wani labarin kuma, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya mayar da martani ga kalaman da aka jiyo shugaban G-5 kuma gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi yayin ganawa da manema labarai a jihar Bauchi kwanakin baya, inda ya ce kungiyar tana nan daram kuma kofa a bude don yin sulhu.
A cikin wata takardar manema labarai da aka akalanta ta da, ‘Atikun, an jiyo cewa yana maraba da samun zaman lafiya da kungiyar ta Wike’ wanda mai baiwa Atiku shawara kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, ya sanya wa hannu, wadda LEADERSHIP ta samu a ranar Juma’a.
Tsohon mataimakin shugaban Nijeriyar ya yi na’am da rahotannin da ke cewa Gwamna Wike da kungiyarsa sun yi na’am da su warware matsalolin da shi.
“Atiku Abubakar ya kuma bayyana kudurinsa na yin shawarwarin da za a warware rikicin bisa amana da kuma share fagen samun karin karfi da hadin kan PDP.
“Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya ya lura cewa ba a taba rufe kofofin sulhu da Gwamna Wike da kungiyarsa a kowane lokaci ba.
“Ya kuma umurci kowane shugaban jam’iyyar da magoya bayansu ba tare da la’akari da ra’ayinsu ba da su kasance masu bude ido tare da marawa tsarin warware matsalolin da ke faruwa,” in ji Ibe.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa jam’iyyar PDP tsagin G-5 ta yi ta takun-saka da Atiku da shugabannin PDP tun bayan fitowar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023, kan ci gaba da zaman Dr. Iyorchia Ayu a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa.