Shugaban hukumar yaki da rashawa da dangoginta (ICPC) na jagorantar hadin guiwa da hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta kasa (NITDA) wajen yin amfani da fasahar zamani domin dakilewa da toshe kafofin rashawa da babakere da dukiyar al’umma a Nijeriya.
Shugaban ICPC, Musa Aliyu, SAN, a yayin zaman domin kulla kyakkyawar alakar aiki da NITDA da ya gudana a cikin makon jiya, ya ce, babu makawa, rungumar dabarun amfani da hanyoyin fasaha na zamani za su taimaka sosai wajen rage kaifin rashawa a kasar nan.
- Zargin Badaƙala: Sadiya Ta Kai Kanta Ofishin EFCC
- Kotu Ta Dakatar Da EFCC, ICPC, DSS Daga Tsare Sanata Yari
Ganawar ta kuma kai ga bada daman hada wata kakkarfar kwamiti da zai kara kyautata alaka a tsakanin hukumomin biyu, wanda a cewar masu ruwa da tsakin, wani mataki ne bullo da sabbin dabarun zamani da hikimomi wajen magance illa da barnar rashawa da cin hanci a Nijeriya.
Shafin Kimiyya da fasaha na LEADERSHIP Hausa ya labarto cewa, ita dai wannan alakar an shirya da tsarata ne tun zamanin mulkin tsohon shugaban ICPC, Farfesa Bolaji Owasanoye, a 2021 da nufin taimakawa kokarinsu wajen yaki da rashawa da toshe haramtatun hanyoyin hada-hadar kudade.
A sanarwar manema labarai da kakakin ICPC Azuka Ogugua ya fitar, ya ce, shugaban ICPC na yanzu, Aliyu ya ziyarci NITDA ne domin tsara sabbin dabarun yaki da rashawa, maida hankali wajen amfani da fasaha domin jagorantar nasarorin ayyukan ICPC kan yaki da rashawa da cin hanci.
Aliyu na cewa, “Da dukkanin amfanun kowace bangare, rungumar dabarun fasaha shi ne muhimman matakin yaki da kuma dakile rashawa. Alakarmu da NITDA na da manufar taimakawa ICPC ne wajen tafiya da zamani, inganta gaskiya, rikon amana, dakile kafofin barnata dukiyar jama’a da kuma inganta amincewar jama’a ga masu jagorantarsu ta hanyar rage kaifin rashawa.
“Yaki da rashawa ba tare da amfani da fasaha ba ba zai yiyu ba a wannan lokacin. Babban nauyin da ke kan ICPC sun hada da har da dakile aikata rashawa, bincike, da gurfanawa. Fasaha zai taimaka mana sosai wajen gudanar da wadannan ayyukan da suke gabanmu,” shugaban ICPC ya shaida.
Shi kuma a nasa bangaren, darakta janar na NITDA, Kashifu Abdullahi, ya nuna kwarin guiwarsu na taimaka wa ICPC wajen cimma manufofin kyautata aiki da ta sanya a gaba.
Ya nanata muhimmancin da ke akwai wajen saukaka aiki da kyautata aikin ta hanyar amfani da fasaha, ya ce, za su kara zaunawa su bullo da muhimman hanyoyin da za su taimaka wa hukumar matuka.