Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (ICPC) a cikin makon nan ta ce, sashinta na bin diddigin ayyukan mazabu da ayyukan da aka yi watsi da su, ya bi sawun ayyukan naira biliyan 219.844 da rassa da hukumomin gwamnatin tarayya 176 suka gudanar bisa rashin nagarta da rashin inganci.
Shugaban hukumar, Dakta Musa Adamu Aliyu, shi ne ya shaida hakan a lokacin da ke ganawa da ‘yan jarida a Jihar Legas.
- ASUU: Jami’ar Abuja Ta Tsunduma Yajin Aiki
- NAHCON Ta Ayyana 15 Ga Watan Mayu Ranar Tashin Alhazan Farko Daga Nijeriya
Ya ce, aikin bin dindigin ya maida hankali ne kan muhimman bangarori da suka shafi ilimi, noma, kiwon lafiya, gine-gine da manufar tabbatar da cewa kudaden gwamnati na tafiya kai tsaye wajen amfanar da talakawan Nijeriya ba wai su sulale ta inda ba su kamata ba.
Ya ce, an fara gudanar da aikin ne a watan Nuwamban 2023, kuma ya ci gaba da gudana a farkon zangon 2024 da ya kunshi muhimman bangarori a jihohi 26 ciki har da birnin tarayya Abuja.
Dakta Adamu ya kara da cewa a zangon farko na aikin sun bi sawun ayyuka 1,721 da gwamnati ke daukan nauyi, inda kuma bincike ke ci gaba da gudana kan wasu da aka gano an tafka rashin gaskiya kamar wadanda ba a ma gudanar da ayyukan ba, ko yin coge, ko wadanda aka yi watsar da aikin nasu da wadanda ba a kamma-la ba, hadi da ayyukan da aka shirya sama da fadi da kudaden da aka ware domin gudanar da su.
Ya ce, za su tabbatar sun taimaki gwamnati wajen kwato kudaden da aka sace da yin sama da fadi da su.