Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC ta fara binciken tabbatar da matsayin aiwatar da ayyuka a Mazabun Majalisar Tarayya 10 wadanda Gwamnatin Tarayya ta bayar da kwangilar aiwatar da su kan sama da naira miliyan 355 a Sakkwato.
Binciken gano matsayin ayyukan yana a karkashin rukuni na biyar na bankado ayyukan Mazabun Tarayya da Hukumar ICPC ke aiwatarwa a Jihohi 21 wadanda aka bayar da aikin su a cikin Kasafin Kudin 2021.
Jagoran tagagar Hukumar ICPC Mista Sa’idu Yahaya ya bayyanawa manema labarai a yau cewar za su gudanar da binciken ayyuka a yankin Majalisar Dattawa biyu da Mazabun ‘Yan Majalisar Tarayya biyar. Daga ciki akwai Mazabar Sakkwato ta Arewa wadda Sanata Aliyu Wamakko, Mataimakin Shugaban Kwamitin Yaki da Rashawa a Majalisar Dattawa ke wakilta.
“An bayar da kwangilar ayyukan a kan naira miliyan 355, 391, 657. 95 tare da tsammanin za a kammala su bakidaya. Tawagar mu ta kunshi wakilan ICPC, kungiyoyin farar hula da ‘yan jarida wadanda duka za su bi diddigin ayyukan.”
“Hakan na da manufar gano ayyukan, yanayin ayyukan da adadin kudin da aka kashe a ayyukan da adadin kudin kwangila, ‘yan kwangila, kudaden da aka biya da gano mutanen da suka jagoranci ayyukan.” Ya bayyana.
A cewarsa tawagar za ta kuma binciko kamfunan da suka yi ayyukan, binciken ko an cika sharuddan ayyukan da kudaden haraji. Ya ce za su duba kima da muhimmancin ayyukan ga al’ummar da aka yi domin su.
Ayyukan da za a gudanar da binciken gano su sun hada da samar da motoci a yankin Majalisar Dattawa a Sakkwato ta Gabas da Sanata Ibrahim Abdullahi Gobir ke wakilta da babura a Mazabar Sakkwato ta Arewa da Sanata Aliyu Wamakko, tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato ke wakilta.
Haka ma akwai binciken gano tabbatar da rarraba babura 188 a Mazabar Gwadabawa/Illela da Hon. Abdullahi Salame ke wakilta a Majalisar Wakilai.
Sauran sun hada da samar da takin zamani na NPK da fanfunan ruwa a Mazabar Kware/Wamakko da shirin karfafawa al’umma kan aikin gona a Mazabar Tarayya ta Bodinga/Dange/Shuni/Tureta wadda Hon. Balarabe Kakale ke wakilta a wa’adin zango na farko.
Tawagar ta riga ta ziyarci wasu daga cikin ayyukan da aka aiwatar a Mazabar Tarayya ta Sakkwato ta Arewa/Sakkwato ta Kudu da Bodinga/Dange/Shuni/Tureta.