Kamfanin samar da wutar lantarki na Japan dake sarrafa tashar samar da wutar lantarki ta karfin nukiliya ta Fukushima, ya yi aikin gwajin na’urorin zubar da ruwan dagwalon nukiliya cikin teku a kwanan baya. An ce kila ana share fagen gudanar da wannan aiki ne kafin karshen wannan wata.
Yayin da take fuskantar rashin jin dadi da kin yarda daga al’ummar duniya, gwamnatin Japan ta yi ikirarin cewa, ruwan da ta sarrafa bai gurbata ba, har ma ta kirkiro wani mutumin Cartoon na sinadarin Tritium wanda ke iya illata lafiyar jikin mutum, don rage damuwar al’umma.
Ban da haka, ta taba samar da kayayyakin teku ga mahalarta wasan Olympic na lokacin hunturu na 2021 da aka yi a kasar, da taron kolin G7 da aka yi a Hiroshima, don tilastawa saura amincewa da matakinta.
Amma, al’ummar duniya ba su amince da ita ba. A gun taron tattaunawa na Shangri-la da aka yi a Singapore kwanan baya, ministan harkokin cikin gida da bulaguro na kasar Fiji, Hon. Pio Tikoduadua ya yi suka da kakkausar murya cewa: “Japan ta yi ikirarin cewa, ruwan dagwalon nukiliya da ta sarrafa bai gurbata ba, to amma idan haka ne me yasa ba ta ajiya shi ba?”
Gwamnatin Japan na kokarin mai da baki fari kan batun ruwan dagwalon nukiliya, saboda kowa ya sani, idan an zubar da ruwan dake kunshe da sinadinai fiye da 60 masu gurbata muhalli a cikin teku cikin tsawon shekaru 30, ba shakka zai illata muhallin teku, da lafiyar jikin daukacin Bil Adama.
Muhallin teku muradun kasa da kasa ne, kuma zubar da ruwan cikin teku da Japan za ta yi, ba wai ya shafi Japan ita kadai ba ne.
Dole ne Japan ta daina yin yaudara kan matakin, ta sauke nauyin dake wuyanta na kasa da kasa, da dakatar da zubar da ruwan cikin teku, da ma fitar da wata hanyar da ta dace don daidaita wannan batu, tare kuma da amincewa a sanya ido a kan ta.(Mai zana da rubuta:MINA)