Zargin Gwamnatin Tarayya Kan Watsi
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ƙaryata wani rahoto da ke cewa wai ya ce a yi watsi da damuwar da Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya yi kan batun tsaro.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafin sa na X, Idris ya ce labarin ba gaskiya ba ne ko kaɗan, kuma ya buƙaci kafafen yaɗa labarai da su riƙa tabbatar da sahihancin rahotannin su.
- Basukan Da Nijeriya Ke Biya Sun Karu Zuwa Naira Tiriliyan 13
- Hisbah Ta Lalata Katan 51 Na Giya a Jihar Yobe
Ya ce: “Ina so in fayyace cewa ban taɓa yin watsi da damuwar da Gwamna Zulum ya bayyana kan tsaro ba, ko kuma wai na ce a yi watsi da shi. Wannan ƙarya ce tsagwaron ta. Don Allah a yi watsi da rahotannin da ke cewa na yi hakan.
“Ina roƙon dukkan kafafen yaɗa labarai da su riƙa bayar da rahotanni bisa gaskiya.”
Ministan ya ce maganar da ya faɗa da farko wadda ba a ruwaito ta a daidai ba ita ce:
“E, lallai an samu cigaba a harkar tsaro a sassa daban-daban na ƙasar nan, ko da yake ba a kawar da duk wani aikin tashin hankali gaba ɗaya ba.
“Hukumomin tsaro suna aiki ba dare ba rana don tabbatar da cewa an shawo kan matsalolin da ake da su a wasu sassan Jihar Borno da wasu wurare.
“Haɗin gwiwar da muke gani tsakanin hukumomin tsaro, musamman a shekaru biyu da suka wuce, da kuma gagarumin zuba jari a kayan aiki da na’urorin zamani da ake yi, yana nuna yadda Gwamnatin Tarayya take ɗaukar batun tsaro da matuƙar muhimmanci.
“Gwamnatin Tinubu tana da ƙwarin gwiwar kawar da ayyukan ‘yan bindiga da ta’addanci a faɗin ƙasar.
“Nasarorin da hukumomin tsaro suka samu a cikin watanni 18 da suka wuce suna nuna cewa lallai Nijeriya tana komawa daidai a hankali a hankali.
“Gwamnati tana kira ga kowa da kowa, musamman gwamnatocin jihohi, da su haɗa hannu wajen kawar da ragowar ‘yan ta’adda da masu aikata laifuka a duk inda suke.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp