Wata kwararriya ta bayyana a jiya Laraba cewa, aiwatar da aikin da zai kai ga cin gajiyar ilimi a jihar Xinjiang ta kasar Sin, ya kai matsayi mafi girma a tarihi, kama daga karatu a matakin ajujuwan reno, zuwa karatun firamare da na aji uku na midil na wajibi, da karatun sakandare, da karatun jami’a da na koyon sana’o’i.
Kungiyar nazarin hakkin dan Adam ta kasar Sin a ranar Laraba ta gudanar da wani taro mai taken “zamanantar da salon kasar Sin da kare hakkin bil Adama” a gefen taron kolin kwamitin kula da harkokin kare hakkin dan Adam na MDD karo na 45.
- Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara…
- An Maido Da Huldar Diplomasyiya Tsakanin Sin Da Nauru, CMG Ta Bude Ofishinta A Nauru
Remina Xiaokaiti, kwararriya a fannin harkokin kare hakkin bil’Adama na jami’ar Xinjiang ta bayyana cewa, a gun taron na ranar Laraba, an tabbatar da cikakken ‘yancin neman ilmi ga dukkan kabilun jihar Xinjiang, kuma nasarorin da ba a taba ganin irinsu ba a fannin tattalin arziki da zamantakewar al’umma a can, sun kara faranta zukatan jama’a. .
Xiaokaiti ta ce a baya-bayan nan ta gudanar da wani bincike kan cibiyoyin ilimi a birnin Kashgar, inda ta gano cewa akwai tsarin bayar da ilimi na shekaru 15 kyauta a garuruwa da kauyukan da ke wurin, kuma a halin yanzu gwamnatin kasar ce ke biyan kudin abincin dalibai. (Yahaya)