Assalamu alaikum iyaye barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa a shafinmu mai farin jini na Raino Da Tarbiyya.
Akwai iyaye da dama wanda ke yi wa yaransu rowa, musamman lokaci zuwa lokaci na sama musu dan wani abin kwadayi.
- Kasar Sin Na Adawa Da Matakin Amurka Na Keta Ka’idojin Fitar Da Kayayyaki
- Kasar Sin Ta Sake Bayyana Matsayinta Kan Rahoton Ofishin OHCHR Dangane Da Jihar Xinjiang
Yaro yana da dabi’ar ganin abu ya ji ya ba shi sha’awa ko kwadayi koda kuwa a in ba wani a in azo a gani bane sai ya saka ransa a kai.
Anan yana da kyau iyaye su kasance masu kula da hakan, domin yana haifar da illa da matsala kwarai ga yaran. Iyaye mu kula wurin sayo abin da kanmu mu basu, hakan zai hanasu gani a wani har su dora ransu a kai.
Kar mu saba da basu kudi, amma mu saba da shigowa da abin gida, kamar irin su kayan kwalam masu saukin kudi.
Amma wasu iyaye kan yi sakaci wurin kyale yaran sai dai su hango a wurin wasu, hakan ka jefa yaro ga zama mai kwadayi na sosai ko kuma ya fada yin data son kashe wa kansa wannan kwadayin.
Wani lokaci ba yaro kawai me bukatar hakan ba, hatta iyaye mata na da bukata sai dai da me su suna da girma da hankalin da basu iya dauke kansu da ga hakan ne.
Mu sani yaro shi ba shi da wata matsala illa yadda ya taso wani lokaci shi ke haifar masa da matsala, duk da wasu yaran ba abin da suka rasa amma sai su tashi a lalace saboda sharrin abokai ko sharrin zamni.
To yana da kyau mu kula wurin kashe kwadayin yaranmu gudun kar su fada a wata matsala, daga karshe mu hada da addua.