Ma’aikatar kula da cinikayya ta kasar Sin, ta bayyana adawa da matakin Amurka na keta matakan fitar da kayayyaki na kasar, domin hana fitar da kananan na’urorin laturoni na Semiconductor zuwa kasar Sin.
Kakakin ma’akatar Shu Jueting ne ta bayyana haka, yayin taron manema labarai na jiya, domin mayar da martani ga matakin da Amurka ta dauka a baya-bayan nan, na hana fitar da naurorin kirar Nvidia, samfuran A100 da H100 zuwa kasar Sin.
Ta ce irin wannan yunkuri ya sabawa ka’idar takara cikin adalci da kuma ka’idojin cinikayya da tattalin arziki na duniya.
Haka kuma zai illata hakkoki da muradun kamfanonin kasar Sin, har ma da na kamfanonin Amurkar.
A don haka, ta ce ya kamata Amurka ta dakatar da tafka kura-kurai da take yi nan take, ta samar da yanayi mai kyau na kasuwanci ga kamfanonin Sin da na sauran kasashen waje, ta kuma aiwatar da abubuwa da suka dace da daidaita tattalin arzikin duniya. (Fa’iza Mustapha)