• English
  • Business News
Thursday, May 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Illolin Ta’ammuli Da Miyagun Kwayoyi Tamkar Makaman Kare Dangi Ne

by Mustapha Ibrahim
2 years ago
in Zamantakewa
0
Miyagun kwayoyi
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Ina ganin haka ce ta sa tun shekaru aru-aru, ina digirgire in hau katako, ko teburi, in kunna Rediyon mahaifiyarmu (rahamar Allah ya je mata) da sauran al`ummar Annabi, nake jin wata waka ta wani mawaki mai suna BIBIYO KONKO a wakarsa da yake cewa “don Allah samari ku daina shan kwaya don shan kwaya masifa ce, takan sa mutum ya lalace!” Haka ma akwai wani mawakin Tangale mai suna LAMBALA a wakarsa da yake cewa, “Shan Wiwi da kwaya sun dauka gaye ne!”

Koda yake zai wuya a ce wadanan fasihan mawaka na suna raye, amma dai sun nuna basira da kishin tarbiyar matasa, duk da yake wasu ba su ji rokon Bibiya Koko ba, kuma wasu matasan sun dauka gaye ne ba gaye ba ne, gidadanci ne ba zan ce kauyanci ba, domin an ce duk asalin birini daga kauye ya fara kuma ba, a raina kauye, ko ko binni domin ko ba komai albarkatun gona na abinci ma fi yawa daga nan yake.

Mu dawo kan maganar illar ta`amali da miyagun kwayoyi ko shansu, ko dillancinsu sun yi kama da makamun kare dangi in wani mai karatu ko wani masani ya ce sun fI hatsari kan makamin kari dangi, ba zan mai musu ba. Saboda yana da hujja, idan ana maganar kare dangi dole a ba da misali da abin da ya faru a 1945 a Japan a harin antomic bom,na Hiroshima da Nagasaki, wanda aka ce fadawarsa ke da wuya ya kashe mutum 80,000 daga baya tiririnsa kuma ya kara kashe mutum fiye da dubu 10 suka kwanta dama.

Ka ga makamin kare dangi na da mumunar illa, amma ta`amali da miyagun kwayoyi ya yi kama da makamun kare dangi domun al`ummar da take sha, ko ta`amali da miyagun kwayoyi ko dillacinsu, to duka ba mai kai labari ko da kowa da ransu, za su ga mumunan karshe.

Mumunan sakamako kuma, ko suna raye to suna mace ne, kamar yadda bom ke kashe muta ne, domun rayuwa ce mara amfani tako wace fuska, dan haka akwai ila da illoli ga wannan dabi`a da Nijeriya, take da hukuma kusum da guda ta NDLEA ta yaki da wannan dabi`a da muka zayana kuma ba shaka kowa ya san wannan hukuma.

Labarai Masu Nasaba

Shirye-shiryen Bukukuwan karamar Sallah

Muhimmancin Karfafa Iyali Wajen Sadaka A Watan Ramadan

Kafunmu shiga magana a Nijeriya, kai tsaye bari mu kali irin illolin da ta`amali da shan miyagun kwayoyi da dillancinsu, ya yi wa siyasar duniya kaca-kaca dubi kasar Kwalambiya, wanda dilalan mugan kwayoyi ne ke juya kasar, wannan ne ma ta sa ake ganin kasa Kwalambiya, na daya daga cikin sansanin mugan dilllan kwayoyi na duniya in har bayanai da bincike ya tabbata akan abun da ake bayana kasar Kwalambiya, haka ne, ga kasar Makziko, na daga cikin kasashen da ake zargi da irin wadanan abubuwa marasa dadi, domun in ba manta ba.

Labari da ya fito ma fi karfi daga makziko a ranar karshe ta tsohuwar shekara ta 2022 shi ne wasu da ake zargi da ta ammali da mugan kwayoyi sun fasa gidan kurkuku ko gidan kaso, ‘yan uwansu masu yawa sun arce, ka ga wannan ya nuna Barazana ga duka da oda aduk inda mashaya ko dilalan kwaya sukayi yawa inba duka da oda akwai matsala a rayuwa, da barazanar zaman lafiya, haka an rawaito a kasar Senigal wasu ‘yan majalisa biyu alkali ya yanke musu hukuncin wata shida a gidan gyaran hali da biyan tarar saifa milliyan biyar kan mangare wata mata yar majalisa a majalisar kasar, any aba kwaya suka sha ba.

A Nijeriya, bayanai sun nuna cewa hukumar NDLA ta kama mashaya ko masu ta`amali da mugan kwayoyi sama da dubu 18 a shakara biyu rak wanda za ka kira wannan nasara ce ga al`umar kasa ba ga hukumar ba kadai domun ko a ranar 25 ga watan daya gabata anzargi wani jami`in tsaro da kashe wata lauya mai juna biyu any aba kwaya ba ya sha ba. Wasu yan uwan majinyata sun kaashe likita a jihar Dalta kan zargin litan da mutuwar dan`uwansu duk dai a wannan lokaci zai wahala a aikata mumunan laifi ba a sha kwaya ba.

Idan ka dawo kano labari mai faranta rai shi ne cewa kano da ake ganin na kan gaba wajen shan miyagun kwayoyi yanzu abun na raguwa sosai a kano na samun cigaba wajen raguwar wannan dabia kamar yadda wadanda su kai buncike a farko na cewa wai kano na ga ba, kuma su ne suka tabbatar da cewa kano na cigaba wajen samun nasarar da dakile sha da ta`amali da miyagun kwayoyi, musamam in aka yi la`akari da cewa a baya can akwai bayanai na masana wannan harkar cewa akwai kimanin muta ne miyan biyu da ake zargi da sha da miyagun kwayoyi a kano, sun ce Kenan duk cikin mutum shida akwai mutum daya mai shan kwayar da ba likita ne ya rubuta masa b,amma dai Kano ana kokari mutuka na dakile shan miyagun kwayoyi da ta ammali da su kamar yadda hukumomin jahar ke bayanawa a koda yaushe.

Illar shan miyagun kwayoyi sun taba ko ina na rayuwar dan`adam tun daga kan lafiyarsa da tunaninsa domun kowa ya san akwai wata halita a kwakwalwa da ake kira MEDULLA OBLONGATA kamar yadda na fahince ta a daya daga cikin darusan da muka yi na Biology kuma nassan dole tanada alaka da wani bayani duk dai a darsun sanin halitun da ake cewa da ke aikin kwakwalwa ne ake samun samun wata Jimla ta turanci Hearing And Interpretation of Speech ma`ana ita ce mai ji da fahimtar abu da kuma bayana shi na dan`adam, idan kuma ban fahimci haka ba, to masana ko likitoci sa gyara wannan kuskuran inda shi.

In kuma haka ne dama shi dan’jarida kullum na tare da masana iri-iri da sauransu da ake zanta wa da su dan ilimantar da kanasa da sauran mutane a kan fannoni daban-daban to tunda shan kwaya likitoci sun tabbatar yana gurbata tunani to ashe ko sham miyagun kwayoyi na da ban ban hatsari ga lafiyar dan`adam.

Illar shan miyagon kwayoyi ga tattalin arziki wanda kwaya ta bugar ba zai taimaki kansa ba, ba zai taimaki al`umar sa ba, ba zai taimaki kasar sa ba, aikuwa akwai ila babba,a ta`ammali ko sha miyagun kwayoyi a rayuwar dan`adam domin ba za asa wanda kwaya ta bugar ba shugabanci ba, na siyasa ko na addini ba, duk wani abu na yabu da ake san ci gaba masu shan miyagun kwayoyi indai gaskiya ne ba za su zama masu jagorantar abun kirki ba.

Wani masanin tahiri da siyasar duniya ya ce duk wata kasa ko wata daula da ake san ruguza ta daga nagarta da kyakyawan shugabanci zuwa lalacewa ta rashin bun doka da oda to a yake ta da cusawa matasanta shan miyagun kwayoyi shi ke nan ankarya ta ammata illa fiye da da illar da Atomic Bom ya yiwa Japan kimanin shekaru 78 da suka wuce domin duk da illar duk da aka jefawa Japan a yakin duniya na biyu japan dai yanzu na daga cikin kasashe masu ci gaban kimiyya da fasaha a duniya ashe kuwa shan miyagun kwayoyi ko ta’ammali da su ya yi kama da makamun kare dangi koma ya fi illa.

Akwai dai hanyoyi da masana daban-daban suka zaiyana wajen dakile wannan matsala a kowace jiha ko koma a ko wace kasa da ta samu kanta a wannan annoba ko bala`i ma fi muni wajen ruguza al`umma a addininta da iliminta da al`adunta da siyasar ta da tsaronta shi ne daukar mataki na kame dillalan miyagon gwayoyi da gurfanar da su gaban shari`a da yi musu hukunci dai dai da abun sukayi na amfani da mugun makami a kan al`uma na dabiar sha ko dillancin mugan kwayoyi su kuma wadanda aka kama da sha abun da ya kamata amusu a tsaresu a zaunar da su a sasu a layi na daina sha da kuma nuna musu illar shan mai makwan mashaya su zama masu amfani a kasar su da al`umarsu da dai sauran hanyoyi wanda hukumomin haki da sha da ta’ammali da dilancin mugan kwayoyi suka sani kuma suke kokari a kai sai dai kawai a yi abun da yake akan doka ba sani ba sabo domun babu wanda ya fi karfin doka ta hukunta shi sai mutum biyu wanda bai karya ta ba, sai kuma mai tabin hankali Allah shi kiyaye, ya ba mu lafiya ya raba al`umma da shan miyagun kwayoyi da ta’ammali da su.

Daga MUSTAPHA IBRAHIM KANO.
Email:[email protected]


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Karamin Yaro Ya Harbi Malamarsa Da Bindiga A Amurka

Next Post

Ana Ta Kokarin Batar Da Kudaden Da Muke Zargin Gwamnan CBN Ya Sha Kwana Da Su —Gudaji

Related

‘Yansanda Sun Hana Hawan Sallah A Kano Saboda Tsaro
Taskira

Shirye-shiryen Bukukuwan karamar Sallah

2 months ago
Muhimmancin Karfafa Iyali Wajen Sadaka A Watan Ramadan
Taskira

Muhimmancin Karfafa Iyali Wajen Sadaka A Watan Ramadan

2 months ago
Me Ke Kawo Saurin Talaucewa Bayan Kammala Aikin Gwamnati?
Taskira

Me Ke Kawo Saurin Talaucewa Bayan Kammala Aikin Gwamnati?

3 months ago
Maganin Zubewar Mama Da Yadda Ake Gyara Shi 
Taskira

Yadda Mata Ke Daukar Yara Don Taya Su Aikin Gida

5 months ago
Yawaitar Ambaliyar Ruwa: Ina Mafita?
Taskira

Yawaitar Ambaliyar Ruwa: Ina Mafita?

8 months ago
Me Ya Fi Ci Wa Samari Da ‘Yan Mata Tuwo A Kwarya Game Da ‘Ramadan Basket’?
Taskira

Me Ya Fi Ci Wa Samari Da ‘Yan Mata Tuwo A Kwarya Game Da ‘Ramadan Basket’?

1 year ago
Next Post
Ana Ta Kokarin Batar Da Kudaden Da Muke Zargin Gwamnan CBN Ya Sha Kwana Da Su —Gudaji

Ana Ta Kokarin Batar Da Kudaden Da Muke Zargin Gwamnan CBN Ya Sha Kwana Da Su —Gudaji

LABARAI MASU NASABA

UTME

ASUU Ta Yi Barazanar Maka JAMB A Kotu Biyo Bayan Samun Mummunan Sakamako A UTME

May 14, 2025
Xi Jinping Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Colombia Da Chile

Xi Jinping Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Colombia Da Chile

May 14, 2025
Gwamnatin Tarayya Da Majalisar Dokoki Za Su Haɗa  Gwiwa Kan Sake Duba Dokar Laifukan Intanet — Minista

Gwamnatin Tarayya Da Majalisar Dokoki Za Su Haɗa  Gwiwa Kan Sake Duba Dokar Laifukan Intanet — Minista

May 14, 2025
Yadda Kasar Sin Ke Kokarin Gina Tashar Bincike A Sama Da Tubalin Kasar Duniyar Wata

Yadda Kasar Sin Ke Kokarin Gina Tashar Bincike A Sama Da Tubalin Kasar Duniyar Wata

May 14, 2025
gaza

Kasafin Kudi Na Naira Tiriliyan 1.78 Na Abuja Ya Tsallake Karatu Na Biyu A Majalisa

May 14, 2025
Kasar Sin Za Ta Inganta Cikakken Tsarin Fitar Da Ma’adanai Zuwa Ketare Don Kiyaye Tsaron Kasa

Kasar Sin Za Ta Inganta Cikakken Tsarin Fitar Da Ma’adanai Zuwa Ketare Don Kiyaye Tsaron Kasa

May 14, 2025
Tinubu Ya Yaba Wa Sule Lamiɗo A Taron Ƙaddamar Da Littafin Tarihin Rayuwasa

Tinubu Ya Yaba Wa Sule Lamiɗo A Taron Ƙaddamar Da Littafin Tarihin Rayuwasa

May 14, 2025
Manyan Ayyuka Guda Biyar Za Su Raya Makomar Al’ummomin Kasar Sin Da kasashen Latin Amurka Da Caribbean Ta Bai Daya

Manyan Ayyuka Guda Biyar Za Su Raya Makomar Al’ummomin Kasar Sin Da kasashen Latin Amurka Da Caribbean Ta Bai Daya

May 14, 2025
Yadda Aka Gina Ofishin ‘Yansanda Na Zamani A Abuja

Yadda Aka Gina Ofishin ‘Yansanda Na Zamani A Abuja

May 14, 2025
JAMB Ta Amince Da Maki 140 Da 100 Mafi Karancin Maki Na Shiga Manyan Makarantu

JAMB: Tangarɗar Na’ura Ne Ya Haifar Da Gagarumar Koma Baya A Sakamakon UTME Na 2025

May 14, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.