A ƙoƙarin daƙile bautar da yara a Nijeriya, Hukumar Kwadago ta Duniya (ILO) ta shirya taron horaswa daga ranar 18 zuwa 27 ga Fabrairu, 2025, a jihohin Neja da Osun, domin karfafa gwuiwar masu ruwa da tsaki a yaƙi da wannan matsala.
Taron ya haɗa da wakilan gwamnati, ƙungiyoyin ƙwadago, shugabannin al’umma da kwamitocin da ke sa ido kan bautar da yara, inda aka ba su kayan aiki don taimakawa wajen gano da kuma kai rahoton irin wadannan ayyuka.
- Yadda Za A Kare Yara Daga Barazanar Intanet
- Hajji: An Bukaci Gwamnoni Da Su Gyara Sansanin Alhazai A Jihohinsu
Daraktar ILO a Nijeriya, Dr. Vanessa Phala, ta bayyana cewa wannan shiri na ACCEL Africa yana nufin haɗa kai da hukumomin da suka haɗa da Ma’aikatar Kwadago, Ma’aikatar Noma da ta Ma’adinai, domin aiwatar da dokoki da tsare-tsare na kare yara daga bautar da su.
Shirin zai kuma mayar da hankali kan bincike a yankunan da ake haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, tare da samar da mafita irin su kariya ga yara, tallafi na kuɗaɗen, kiwon lafiya da kuma samar da ayyukan yi ga matasa.
Ana sa ran wannan taro zai taimaka wajen kawo ƙarshen bautar da yara, musamman a ɓangaren hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, da kuma inganta kare hakkin yara a faɗin ƙasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp