A bana ake bikin cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da kungiyar Tarayyar Turai ta EU, ana kuma daf da gudanar da sabon zagayen taron jagororin Sin da EU. Sakamakon hakan, jerin ayyukan cudanya a matsayin koli tsakanin sassan biyu na kara jan hankali.
A baya-bayan nan, an gudanar da dandalin tattaunawa na manyan jami’ai tsakanin Sin da EU karo na 13 a birnin Brussels na kasar Belgium. Kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da shugabannin EU, tare da ziyartar kasashen Jamus da Faransa. Bangaren Sin ya jaddada cewa, bunkasar tafarkin ci gaban alaka tsakanin Sin da EU ya nuna kyakkyawar dangantakar sassan biyu maimakon adawa da juna, kuma hadin gwiwarsu shi ne tushen cimma nasara tsakaninsu. Kazalika, ya yi kira ga Sin da EU da su hada karfi waje guda don samarwa duniya wani yanayi na tabbaci.
Ya ce, matsayin alakar Sin da EU na manyan karfi biyu, kuma manyan kasuwanni biyu, kana manyan wayewar kai biyu, ya shaida damar musaya da hadin gwiwa, ba gare su kadai ba, har ma da dukkanin duniya baki daya. Jimillar karfin tattalin arzikin Sin da EU ya haura daya bisa ukun na duniya baki daya, kana darajar yawan cinikayyarsu ta haura daya bisa hudun ta duniya baki daya. Sassan biyu na rike da manufar cudanyar mabambantan sassa, suna goyon bayan cinikayya marar shinge, da wanzar da tattaunawa da tsare-tsaren gudanarwa kan muhimman batutuwa, irinsu sauyin yanayi da fasahohin AI. A halin da ake ciki, rikicin siyasar yankuna na kara tsananta, an kuma shiga yakin haraji da na cinikayya. Sin da Turai na da nauyi da hakki, da ikon hada hannu waje guda don kare adalci, da nuna adawa da cin zali daga bangare guda, da nuna kin jinin baiwa kasuwa kariya. Kamar dai yadda Sin ta bayyana, idan Sin da Turai sun wanzar da tattaunawa da hadin gwiwa, zai yi wuya a kai ga yin fito-na-fito tsakanin wasu sassa. Kazalika, idan Sin da Turai sun zabi bude kofa, da hadin gwiwar cimma moriya tare, hakan zai sauya salon dunkulewar tattalin arzikin duniya. Idan Sin da Turai sun hada hannu wajen aiwatar da manufar cudanyar mabambantan sassa, duniya ba za ta tsuduma cikin yanayi na hargitsi ba. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp