A yau ma shafin Rumbun Nishadi na tafe da wani babban Jarumi wanda ya shafe kusan shekaru 20 a cikin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, wato Haruna Talle Mai Fata, inda ya yi wa masu karatu karin haske dangane da irin mummunan kallon da sauran al’umma ke yi wa masana’antar Kannywood tare da wadanda ke ciki a jimlace. Jarumin ya bayyana abubuwa masu yawan gaske dangane da abin da ya shafi fina-finan Hausa da kuma masana’ar gaba daya. Ga dai tattaunawar tare da RABI’AT SIDI BALA Kamar haka:
Masu karatu za su so su ji cikakken sunanka tare da dan takaitaccen tarihinka…
Assalamu akaikum warahmatullahi ta’ala wa barakatuhu. Sunana Haruna Talle Mai Fata Sardaunan Samarin Arewa, kamar yadda ake kirana da shi a masana’antar Kannywood da sauran ‘yan kallo gaba daya. Ni dai an haife ni a Jos, iyayena kuma daga Kano gefen Babata wani bangaren daga Kano, wani gefen daga Katsina. Na yi makarantar firamare da Sakandare dina duk a Garin Jos, inda na tafi Bauchi na yi Jami’a, na tsaya a dai-dai deploma. Ina da mata da yara guda hudu, mata uku namiji daya, kuma a yanzu haka ina ci gaba da rayuwata a garin Jos.
Me ya ja hankalinka har ka tsunduma cikin masana’antar Kannywood?
Sana’ar fim sana’a ce wadda za ki ga mafi yawancin mutane idan suka ta so, musamman yara za ki ga sun taso da sha’awar son yin fim. To Gaskiya a gidanmu akwai wanda shi furodusa ne, kuma su ne suka fara yin ma fim a Jos, don in bai zo na biyu ba to zai zo na uku yayanmu ne, shi ya fara yi. Lokacin da ya fara yi sai ya dan kwadaita mun zai saka ni sai na kara jin sha’awar abin, to daga baya kuma ya zo Allah bai ba shi ikon saka ni ba, da ke gidanmu gida ne irin wanda duk wanda ya taso in har za ka iya magana ka iya tafiya, ka iya dagawa ka ajjiye a nan, komai kankantarsa tun da kin ga fata ba ta da nauyi, to kawai yana da sana’a duk sati za a biya shi, shi ne za ki ga kowa da dan kudinsa a hannunsa ko ba yawa, saboda gidanmu gidan kasuwa ne sana’ar babanmu muke, dukka fata muke saya da sayarwa, shi ne na ji kawai gara na yi nawa. A nan ne cikin ikon Allah na nemi wani Darakta da ya ke abokin shi yayan namu ne, Bello Muhammad Bello na bashi aiki ya yi min fim, nan take kuwa ya rubuta wani fim me suna ‘ZUCIYATA’, da ya rubuta ya kawo muka duba na ce ga rawar da zan yi a ciki, ni zan fito a jarumion fim din wato zan jagoranci fim din ya ce a’a! yanzu ya yi sauri ban taba yi ba na ce zan fito a jarumi in bari tukunna na nemi wani wurin a sa ni. Na nemi wasu jarumai a kannywood, da yake shi babban furodusa ne sai suka dan nuna mun na bari idan aikinsa ya zo sai su zo in sun yi masa sai su dan yi mun, kin ga zan samu sauki. To da na jira-na jira kawai sai na nemi shi daraktan na ce kai me ya sa ba za ka yi mun rol din ba?, ya ce zai iya mana shi Bello Muhammad Bello kenan, sai na ce ya yi mun mana, sai ya yi mun. Muka yi fim din cikin ikon Allah muka gama shi sa’annan kuma fim ya samu daukaka, sunan fim din ZUCIYATA, ni na fito a dan gwamna, daga wannan fim din gaskiya na fuskanci cewa zan iya, kuma abin ma da dadi saboda duk inda na je wucewa ana wane-wane, daga nan kawai sai na kara dauko wani ‘rubutun’ me suna ‘HAFSA Ko SAFIYA’ shi ma na yi, nan muka fito da wani jarumi Baba me sakata kenan, na manta ainahin sunan da ake fada masa, jaruminn sakata dai, shi ne nan ma muka je na yi wannan fim din, shi ma na fito irin kai da kai na yi kokari kamar ‘Boss’ da ‘Actor’ na fito rol me yawa fiye da na ‘ZUCIYATA’. Dana saki fim din sai na ga na samu alkhairi sosai, sai na gano cewa wannan fa sana’a ce da za ta rike mutum, Alhamdulillahi kuma gashi ta rike ni duk yawancin abin da na samu a rayuwata kaso casa’in ta wannan sana’ar ce.
Idan na fahimce ka, duk wata gwagwarmaya da wasu ke fuskanta wajen samun damar shiga, kai ba ka fuskance ta ba kenan?
Eh to, gaskiya ban sha wata gwagwarmaya ba, dalili kuwa na farko ina da wadanda sun riga da sun bude min hanya tun da ba wai na zo a matsayina na wanda ban san kowa bane, na zo a matsayina na wanda na san wasu ina da wa ma wanda shi kuma babba ne a masana’antar duk da dai ba wai ta hanyar shi na bi ba, amma kuma zan iya cin alfarmar sa, mutane da yawa za su ce kanin wane ne bari mu yi masa kaza, kuma shi babban furodusa ne sosai. Abu na biyu kuma, ko yanzu-yanzun nan mutum zai yi fim wanda ya zo da kudinsa ya kan fi samun sauki fiye da wanda ya zo ya ce a saka shi, wanda ya zo da kudinsa ma in ya dubi ‘labarin’ ya ce rawa kaza zan yi kuma dole a bar shi ya yi ko da bai iya ba kuwa dole a rika bin shi a hankali. Amma ni na narka kudina na saka ka a fim na ga kana yi baka iya ba, ba ka yin yadda ya kamata kin ga kuwa dolen-dole a samu matsala, ballantana yanzu fim ma ya koma kawai kusanci shi ne kawai ake amfani da shi. Sai kuma wasu daga cikinmu wadanda Allah ya daukaka za ki ga ko ba kusanci ya kira ka “Wane zo ka yi” dalilin sanin fuskarka, amma duk wanda ba a san fuskarsa ba ai mafi yawa kusanci ne ke sawa a saka su, in ba haka ba kuwa gaskiya sai dai mutum in ya zo da kudinshi, Allah kuma ya taimake shi ya bi hanya mai kyau, to shi ne za ki ga bai sha wata wahala ba, amma gaskiya ni ba wata wahala na sha ba.
Ya farkon farawarka ya kasamce, musamman yadda kake sabon farawa a lokacin?
Eh to, gaskiya ban samu wani kalubale game da hakan ba, saboda ina tare da su kusan ko da yaushe masu fim din, dukkansu har manya-manyan masu fim din su kan zo gidanmu su yi fim, ko kuma su zo wajen shi yayanmu, saboda shi babban furodusa ne kamar yadda na fada miki a baya, don ba wani jarumi da yake Kannywood da ba ya zuwa wajensa, don yana da mu’amula da su sosai, saboda shi idan zai yi fim ma ba ya daukar wani in ba babban jarumi ba ko daga ina ne, shi manyan fina-finai ya ke yi. Ana zuwa a dauki wasu bangarori na fim a gidanmu, ana zuwa a dibi kayanmu kayyaki ko wasu abubuwa kin ga ba zai taba zamar mun wani wahala ba. Kuma dadin dadawa ko baka san kowa ba, indai zai zama kai ne me abun za ka samu sauki cikin kaso hamsin. Ni na samu sauki ta haka, tun da fim dina da na fara ni ba wanda ya taba sani a fim, sai da na yi fina-finai na da yawa, ko da ake fim a gidanmu babu wanda ya saka ni a fim, fina-finai na na fara yi kuma sai da na yi ba daya ba, ba biyu ba, ba uku ba kafin wani ya saka ni, hasali ma fim din ko na gidanmu
Ya karbuwar fina-finanka ta kasance a wancen lokacin?
Sun karbu sosai don karbuwarsa ne ma ya sa har na ci gaba, saboda da bai karbu ba ba zan samu karfin gwiwar da na rika sauri dauko wani har ya zamo ina yawan daukar nauyi, wanda a gaskiya a Jos a yanzu ban yi tunanin akwai wanda ya fini yawan daukar nauyin fim ba, mutum daya dai haka mai yawan fina-finai na, ba wai kamfani wannan ya zo ya yi fim dinsa, wancen ya zo ya yi ba. Saboda ni kamfani na ni daya ne, kuma duk fim din da kika gani da sunan kamfanina nawa ne, gaskiya fim dina ya karbu sosai wanda na fara, fina-finaina na farko-farkon sun karbu ko da ma a baya an zo an dan samu matsala, kin ga na saba da fina-finai na karbuwa.
Za ka yi kamar shekara nawa a cikin masana’antar Kannywood?
Zan kai shekara 20, domin na fara fim 2003 karshe-karshenta.
Ko za ka iya tuna yawan adadin fina-finan da ka yi?
Fina-finan da na yi a kasa yanzu haka za su kai kamar guda 50, kuma a yanzu haka ina da Master fim ya kai guda 50 a kasa, akwai; ZUCIYATA na farkon da HAFSA ko SAFIYA, lokacin ana ajjiye fim a cikin irin dan karamin kaset din nan, da aka dawo ajiye fim a ‘hard dribe’ na ke sayensa da yawa na ke sassaka fina-finaina, kin ga tun daga wancen lokacin akwai kamar su; Zuciyata, Hafsa ko Safiya, Kundun Tsari, Farin Sani, Farmaki, Dan Talaka, Ni da Fati, Tawakaltu, Kuyanga, Farida Nabil, duk gasu nan dai suna da yawa fina-finan.
Wanne fim ne cikin fina-finanka wanda ya zamo bakandamuyarka?
Duk fim din da na yi ina sonsa, saboda soyayyar da nake yi mishi ne ya sa na ke yi, in an kawon labarin ko kuma na yi tunanin na yi labari akan abu kaza, in an kawon na ke saka kudi na yi furodusin na yi kayana duk in yin na mutane, amma a yanzu zan iya cewa na fi son Tawakaltu, dalilina kuwa shi ne; Yanzu haka watan da za mu shiga 25/9/2023 in Allah ya kai mu da rai da kafiya na ke so in sake yin ‘Series’ dinsa, kin ga ai akwai fina-finai da yawa kuma duk labaraina ne, amma na fi son Tawakaltu.
Bayan shirya fim da fitowa matsayin jarumi, shin ko akwai wasu abubuwa da ka ke taka rawarsu cikin masana’antar Kannywood?
Eh, na fara da daukar nauyi bayan fitowa a jarumi, da abin ya yi gaba-gaba sai na ga furodusin akwai daga hankali, ka kira wannan wancen ya zame, ka yi nan wannan ya yi nan, sai na dawo na ba wani yaro nawa Umarni ya fara furodusin, ni na ci gaba da tsayawa a matsayina na ‘Edecutibe Producer’, me shirya kenan ba me shiryawa ba. Daga nan kuma sai na fara Bada Umarni, don ba zan manta ba 2006 fim din da na Ba da Umarni na ke ga na uku kenan, don Tawakaltu ma ni na Ba da Umarni, na sami MTN Award na ci ‘Best Barial Actor’, na kan Ba da Umarni, na kan dauki nauyi, na kan Shirya ‘da’, amma a yanzu gaskiya ko fim din waye ni bana shiryawa, saboda bana son in janyo wannan, wannan ya yi nan, sai na bar wani shi ma ya shirya.
Bayan da ka koma Ba da Umarni, ko akwai wani kalubale da ka taba fuskanta, musamman ga su Jaruman wajen ganin sun yi abin da ake bukata su yi na daga fim din, ko kuwa?
Eh, to, gaskiya ban samu wani kalubale ba, na farko da zan yi wannan TAWAKALTU nake ga a kansa na fara Ba da Umarni, to da Allah ya taimake ni kuma na yi shi sai ya zamo ya yi kyau, kuma ya daukaka sosai, to abu na gaba da zan fara yi sai na yi wani ‘DANKA KO DANA, KAYAR BAYA, wannan fina-finan da zan yi sai na kira wo wani babban jarumi wanda yana na daya ko na biyu yanzu a masana’antar, tun lokacin kuma shi ne na daya ko na biyu, na daya ma za a kira shi, shi kuma ya riga ya ga wancen Tawakaltun, don ko da muka hadu a wajen aiki an kira shi ni ma haka, ya ke ce mun kai! Fim din nan gaskiya ka yi kokari amma da gaske kai ka Ba da Umarni, na ce wallahi ni na bayar, ya ce; “Ah! gaskiya ka yi kokari”, Na ce ai akwai fim da za mu yi sai na zo na dauko wannan fina-finan su ma da Allah ya taimaken sai suka karbu, to kin ga duk wanda zan kira ba zan samu wani kalubale na cewa; Ai ban iya ba, ko kuma in mutum ya yi ba daidai ba in na ce mai wane gyara sai ya ki yi ba, kuma daman tun can ma bangaren da na karanta kenan shi ya sa ban samu wani kalubale ba.
Kamar wanne bangare ka fi mai da hankali a kai wajen yin fim, misali kamar; bangaren siyasa ko soyayya da dai sauransu, wanne ka fi karkata?
Gaskiya ni babu irin fim din da ban yi ba, ko bana yi a kamfani na, akwai na soyayya, akwai na daba na marasa ji kenan, ban ma taba na siyasa ba, idan ma barkwanci ne abin dariya akwai, na taba bangarori daban-daban. Amma kamar a yanzu ni ba ni da ra’ayin wani fim ma da bai zama irin wanda zai zama akwai dan jan hankali haka ba.