Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewa yana ci gaba da tuntubar d Rabi’u Musa Kwankwaso da Peter Obi domin neman goyon bayansu ga takararsa.
Atiku ya bayyana haka ne cikin wata tattaunawa da ya yi da BBC Hausa a ranar Talata.
- Sin Na Tsayawa Tsayin Daka Kan Yaki Da Ta’addanci
- TARON LEADERSHIP: Buhari Ya Sauya Fasalin Tsarin Tattalin Arzikin Nijeriya —Ministan Abuja
Ya ce duka su biyun, Obi da Kwankwaso ba su da wata barazana ga nasarar cin zabensa.
“Ban ga wata barazana domin ba muna tare da su (Kwankwaso da Obi). Muna tattaunawa da su, watakila daya daga cikinsu zai zo mu hade,” in ji shi.
Dangane da rikicin jam’iyyar PDP da ya ki ci ya ki cinyewa, ya ce, “Kowace jam’iyya na da irin nata rikicin cikin gidan, muna tattaunawa da su. Yawancin ba a PDP ba ne ko kuma a wasu jam’iyyu kuma tabbas hakan ba zai sa mu fadi zabe ba saboda muna shirye-shiryen tunkarar zabe a yanzu.
“Zaben da ake yi a yanzu ba kamar a baya ba ne lokacin da gwamna zai zabi wanda zai zaba, zaben yanzu yana hannun masu kada kuri’a.”
Dan takarar shugaban kasar, ya kuma yi alkawarin bude dukkan iyakokin Nijeriya idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a wata mai kamawa.