Tsohon MataimakinShugabanƘasa, Alhaji Atiku Abubakar, cikin saƙonsa na ta’aziyya ya bayyana cewa; “Ina matuƙar jimami da alhinin samun labarin rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, mutum wanda rayuwarsa ta kasance cike da ƙaunar ƙasa da sadaukar da kai ga ƙarfafa haɗin kai da martabar Nijeriya,”
“Shugaba Buhari ba kawai tsohon shugaban ƙasa ba ne kaɗai, mutum ne da ya yi wa Nijeriya hidima mai yawa daga fagen fama zuwa matakin jagoranci, ya yi hidima da kishin ƙasa da tsayawa akan gaskiya da da nagarta,” in ji Atiku.
- Rasuwar Buhari Babbar Asara Ce Ga Nijeriya — Obasanjo
- An Tsaurara Matakan Tsaro A Daura Gabanin Jana’izar Buhari A Gobe Talata
Atiku ya ci gaba da baayyana cewa; “Rasuwar Buhari ba kawai rashi ne ba ga iyalinsa da mutanen Daura kaɗai ba, rashi ne ga ƙasa baki ɗaya. Nijeriya ta rasa shugaba nagari da ya ɗauki nauyin jagoranci a lokuta masu wahala, tarihin da ya bari zai sanya a ci gaba da tunawa da rayuwarsa har abada.” Cewar Atiku
Atiku, ya kuma miƙa saƙonsa na ta’aziyya ga iyalansa tare da addu’ar Allah ya basu haƙurin jure rashin da akayi. Ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga mutanen Jihar Katsina da kuma ‘yan Nijeriya gaba ɗaya da fatan Allah ya masa rahma, ya gafarta masa, ya sa Aljannatul Firdaus ce makomarsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp