HAJIYA FATIMA ABDULLAHI DALA mashawarciya ta musamman ga Gwamnan Jihar Kano Kan harkokin Mata da kananan Yara, Shugabar Matan Jam’iyyar APC Ta Jihar Kano, guda cikin Masu rajin ganin Mata da kananan Yara sun amafana da tagomashin Gwamna Ganduje.
A tattaunawar ta da wakilinmu a Kano ABDULLAHI MUHAMMAD SHEKA, Fatima Dala ta bayyana Yadda ta taso cikin Gwagwarmaya musamman bangaren kishin ci gaban Mata, kananan Yara, Jagorancin Al’umma tun daga kasa. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance:
- Kotu Ta Yanke Wa Wani Tsoho Hukuncin Zaman Gidan Yari Na Har Abada Kan Laifin Fyade A Jigawa
- 2023: Ana Rububin Kujerar Ahmed Lawan Bayan Soke Takararsa
Za muso ki gabatar wa da mai karatu kanki da kanki?
Alhamdulillahi, ni dai kamar yadda aka sani sunana Hajiya Fatima Abdullahi Dala, haifaffiyar Jihar Kano a Karamar Hukumar Dala, na taso a Unguwar Dala, nafara Gwagwarmaya tun ina karamar, har kuma tsunduma harkokin siyasa wanda na zama mashawarciya ta musamman ga mai girma Gwamnan Kano a kan harkokin Mata da Kananan Yara sannan kuma a yanzu ni ce Shugabar matan Jam’iyyar APC ta Jihar Kano
Ya ya batun tarihin Gwagwarmayar Rayuwa?
Alhamdulillahi, ni kamar yadda aka sani mun taso cikin kyakkawar kulawar iyaye, wanda hakan yasa muka samu nutsuwa tare da neman yadda za mu taimaka wa Jama’a a dukkan matakin da muka samu kan mu a cikin, na fara Gwagwarmayar kungiyoyi tun daga cikin unguwa, har ta kai na tsundum a cikin harkokin siyasa, wadda na rike mukamin shugabancin mazaba, daga nan na taho karamar hukuma, kokari da Jajircewa ya sa Gwamna Ganduje nada ni mashawarciya ta musamman kan harkokin Mata da Kananan Yara har kuma zuwa yanzu da Allah ya damka shugabancin matan Jam’iyyar APC a hannuna.
Wadanne abubuwa ne suka tsaya miki a zuciya musammana matsayinki na mace kuma mai rike da madafun iko a cikin Jam’iyyar APC a Jihar Kano?
Wannan tambaya ta zama kamar fami a wuri na, amma alhamdulillahi buri na ya cika domin damar da Khadimul Islam Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bani tun daga kan mukamin mashawarciya ta musamman a kan harkokin Mata da Kananan Yara har kuma yanzu da aka zabe ni a matsayin Shugabar matan Jam’iyyar APC ta Jihar Kano, na samu damar Kawo sauyi cikin abubuwan da suka addabi Mata da Kananan Yara, a nan dole na jinjina wa mai dakin Gwamna Farfesa Hafsat Abdullahi Ganduje bisa taimakawar da take wajen shigo da mata cikin harkokin gudanar da Gwamnati, wanda zuwa yanzu kafa fadin kasar nan babu Gwamnan da ya bai wa Mata irin Damar da Gwamna Ganduje ya bai wa Mata a Jihar Kano.
Shaye-shaye na cikin abubuwan da a baya Jihar Kano ta yi kauri suna a kan su, shin kowane kokari Gwamnati ta yi har aka shawo kan wannan matsala?
Ina tabbatar maka da cewa duk Nijeriya babu Gwamnan da ya shirya magance matsalar shaye-shaye kamar Gwamna Ganduje, domin da farko duk cikin Gwamnonin kasar nan shi ya fara samar da mashawarci na musamman kan matsalar shaye-shaye. Mai dakinsa Farfesa Hafsat Ganduje kuma ita ce Matar Gwamna daya tilo da ke Jagorantar kaddamar dakarun yaki da sha tare fataucin Miyagun Kwayoyi mata a fadin kananan Hukumomin Jihar Kano 44, Sannan shi ne Gwamna daya tilo da ya bada Umarnin cewa duk wani jami’in Gwamnatinsa Sai anyi masa gwaji an tabbatar ba shi da matsalar shaye-shaye.
Yanzu haka ‘yan watanni ya ragewa wannan gwamnati a kan karagar mulki, shin kwalliya ta biya kudin sabulu?
Madallah an zo wurin, ina tabbatar maka da cewa, ba maganar kudin sabulu ake a Kano ba, har kudin tutare ma ta biya, domin ayyukan da Gwamna Ganduje ya shimfida wa Kanawa sai an shafe sama da shekara hamsin ana amfanarsu, da farko dai dubi yadda Ganduje ya kawata birnin Kano da manyan gadojin sama da kasa wadanda kaf Nijeriya babu irin su, Kuma shi ne Gwamna daya tilo da bai taba batan watan biyan albashi ba, shi ne Gwamnan da ya kafa cibiyar koyar da sana’o’i irin na zamani wanda Babu irinta wadda aka sa a sunan attajirin Nan can asalin Jihar Kano Aliko Dagote da ma sauran ayyukan da babu su cikin alkawuran daya daukarwa Kanawa, misali karasa ayyukan da Gwamnatocin Baya sukayi watsi da su.
Me kike fatan Jama’a su dinga tuna ki da shi?
Kyakkawar tarbiyar da muka samu daga iyaye da Kuma ayyukan ci gaban Mata da Kananan Yara Wanda Gwamnatin Kano ta sauya rayuwarsu tare Inganta.
Me ki kafi sha’awa ta fuskar abinci?
Ai kasan bakanuwar asali ce ni, saboda mun ta’ammali da abinci Gargajiya wanda muka tashi da shi a al’adun abincin bahaushe, kamar daga tuwo, sinadaran alkama da sauransu.
Sutura fa wacce aka fi sha’awar sanyawa?
Farare da masu launin kore sannan Ina matukar farin dikin ganina cikin hijabi.
Mene sakonki na karshe?
Alhamdulillah, sakona shi ne fatan jama’a su sani ya ba kyauta tukuici, a kara himmatuwa wajen bai wa Gwamna da Gwamnatin Kano goyon baya tare da addu’ar dorewar zaman lafiya. Sannan kowa ya sani lokaci na kara matsowa na Zaben Shekara ta 2023, a yi kokarin karkade kuri’u domin Gwamna Ganduje ya tsayar da na’ibinsa Dakta Nasiru Yusif Gawuna a matsayin dan takarar da muke kyautatawa zaton gadon buzun Ganduje. Sannan muna godiya ga Malamai ma gada Annabawa bias gudunmawar addu’o’in da suke yi wawannan Gwamnati ba dare ba rana.